Wani daga cikin jami’an hukumar motocin jigilar matafiya ta Zamfara, ya shaida wa PREMIUM TIMES HAUSA cewa rahotannin da suka samu daga bakin waɗanda suka tsira a harin ƴan bindiga a titin Kaduna zuwa Abuja ranar Talata ya nuna cewa maharan sun yi matukar nuna rashin mutunci a harin da suka kai.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kaduna Mohammed Jalige ya shaida wa Channels cewa ba dun jami’an tsaro sun yi gaggawar isa wurin da ƴan bindiga suka tare ba, da ta’adin ya fi haka muni.
Jalige ya ce” Jami’an tsaro sun yi arangama da ƴan bindigan. Sun yi bata kashi da su sannan sun fatattake gaba dayan su.
Farouk ya kara da cewa ba wannan mota bace kawai ƴan bindigan suka tare sun tare motoci da dama sannan sun sace mutane, waɗanda kuma kwanan su ya kara suka harbe su.
Titin Abuja -Kaduna ya kusa zama ya gagari jami’an tsaron Najeriya domin ƴan bindiga basu fasa ba, idan suka ɗaga kafa na ƴan kwanaki sai kuma su dawo gadan-gadan.
Sannan har yanzu mutane basu farfaɗo daga fargabar harin da suka kai wa jirgin kasan Abuja ba wand wasu da dama har yanzu na tsare hannun ƴan bindiga.
Discussion about this post