Tsohon shugaban hukumar EFCC Nuhu Ribadu ya bayyana wa dubban magoya bayan sa a jihar Adamawa cewa mutanen jihar za su ragargaji romon dimokuraɗiyyar yadda ya kamata idan har Allah ta kai shi ga nasara ya zama gwamnan jihar.
A cigaba da ganawa da yake yi da ƴaƴan Jam’iyyar APC a kananan hukumomin jihar, Ribadu ya ce daidai da naira ɗaya na talakawan jihar ba zai salwanta ba a karkashin shugabancin sa.
” Sannan kuma ina tabbatar muku da cewa sai mutanen jihar Adamawa sun mori abin da ba su taba mora ba a baya karkashi mulki na. Zan tabbatar da talaka ya dandana gwamnati a ko ina yake a faɗin jihar Adamawa.
” Talakawa da ƴaƴan su za su shaida, kiwon lafiya, Makarantun mu na gwamnati, tsaro da kuma bunkasa tattalin arzikin jihar Adamawa sune za su fi maida hankali akai.
Ɗaya bayan ɗaya zamu kakkabe su duk su zama Tarihi ga mutanen jihar mu.
Nuhu Ribadu na daga cikin fitattun ƴan Najeriya sa duniya take bugun kirji da su a wannan ƙarni wajen tsage gaskiya komai ɗacin ta da kuma nuna kishin kasa da mutanen Najeriya.
Discussion about this post