Ba za’a iya kimanta mahimmancin fasaha a rayuwar dan adam ba. Cigaban da aka samu a sabbin fasahohi sun yi tasiri sosai a rayuwarmu musamman a karni na 21. Fasaha na tasiri kan yadda mutane ke ma’amala da juna a kullayaumin. Za kuma a iya cewa fasaha ta shafi duk wani fanni na rayuwa: kiwon lafiya, illimi, hada hadar kudi da sauransu.
A wasu kasashen duniya an fara samar da hadaka tsakanin fasaha da gwamnati musamman a harkokin zabe. Wannan matakin da aka dauka na amfani da fasaha a tsarin zabe ya yi tasiri sosai. Yau a dkasashen uniya, yawancin hukumomin zabe na amfani da sabbin fasahohi da burin inganta tsarin zabe. Wadansu fasahohin masu saukin sha’ani ne kamar manhajojin rubutu da lissafi sai kuma irin wadanda ke ajiye bayanai masu yawa da daukan hoto da nadan bayanan yanayin kasa.
Gwamnati da siyasa na tasiri a kusan kowani fannin rayuwa kama daga yawan kudin harajin da mutun daya ke biya har zuwa irin kayayyakin da su kan saya dan ayyukan gida da saw a a bakin salati. Zabe kuma shi ne hanyar zaben dan takara zuwa mukami na siyasa. Yana daya daga cikin matakan gangamin siyasa.
Zabuka a Najeriya
Da yawan al’ummar da ta wuce milliyan 210, bayan kowani shekara 4 ‘yan Najeriya ke zaben wakilansu daga matakin karamar hukuma zuwa jiha da matakin tarayya. Hukumar zabe mai zaman kanta INEC wadda ita ce hukumar koli na zabe a kasar ke da alhakin sanya ido kan zaben da kuma tabbatar da sahihancin shi.
To sai dai duk da yunkurin hukumar na gudanar da zabe mai sahihanci ana samun rahotannin magudi wadanda wata sa’a suke janyo rikicin da kan kai ga zubar da jinni. Dan haka, na tsawon shekaru da dama yanzu INEC ke kokarin ganin an yi amfani da fasaha wajen inganta sahihanci da amincin zaben a Najeriya.
A shekarar 2015, hukumar ta yi amfani da smart card readers – wato katin zaben da ke dauke da na’urar tantance jama’a – wajen yin zabe. A lokacin, burinta hudu ne: A tantance katin dan kasa na dindindin wato PVC, wanda ake baiwa masu zabe a wurin jefa kuri’a domin a tabbatar da sahihancinsu. Wani burin kuma shi ne a sami damar tantance wanda ke rike da katin ta yin amfani da zanen yatsu da siffa da kamanin shi a tabbatar cewa bayanan shi na zahiri ne ke jikin katin da ya gabatar.
Haka nan kuma an bayyana cewa an gayyato SCRs domin su raba bayanan duk wadanda aka tantance su yi zabe zuwa rukunnai daban-daban. Wadannan rukunan sun hada da maza da mata da kuma matasa da dattawa.
SCR ta kan tura bayanan masu zaben zuwa INEC ta yadda hukumar za ta iya sake tantance adadin mutanen ta kuma kwatanta shi da wanda jami’an zabe ke aikowa daga wuraren jefa kuri’a domin gano wuraren da aka yi magudi.
A wani rahoton da aka fitar ranar 13 ga watan Satumban 2021, INEC ta ce a shekaru biyun da suka gabata, ta yi amfani da fasahohi da dama wajen tafiyar da zabuka a kasar. Rahoton ya bayyana su a matsayin wuraren ganin sakamakon INEC, wato shafuka daban na zaben ‘yan takara, tantance masu sanya ido kan zabe, tantance kafofin yada labarai da kuma zaben jami’an zabe.
Hukumar ta kuma gabatar da shirin rajistan masu zabe a yanar gizo a matsayin wani fanni na tabbatar da cewa mutane sun cigaba da rajista gabannin zaben, abin da ya sa ma kawo yanzu mutane sama da milliyan suka yi rajista ba tare da wata matsala ba.
Kwanan nan, shugaban INEC, mai kula da kwamitin bayanai da masu zabe, Festus Okoye, yayin da yake hira da Arise TV y ace hukumar za ta yi amfani da tsarin rajistan masu zabe da hanyoyi biyu wato BVAS a zaben gwamnan da za’a yi a jihar Anambara ranar 6 ga watan Nuwamba.
Ya bayyana cewa INEC ta kaddamar da BVAS ne domin a rika ganin sakamakon zabe a kan lokaci.
Mene ne BVAS?
Ana iya kwatanta BVAS a matsayin wani tsarin da zai hada zanen yatsun hannun mutum da siffa da kamanni n fuska dan tantance masu zabe.
Kamar yadda wani babban jami’i ya bayyana, wannan tsarin ya hada matakai uku na zabe. Fasaha ce wadda take abubuwa da yawa a lokaci guda domin ana iya rajista da ita kafin zabe, lokacin zabe kuma ana iya tantance wadanda suka zo jefa kuri’a sa’annan ana iya amfani da ita wajen ganin sakamakon zaben a ranar da zarar aka kammala.
Wannan na’urar za ta hada zanen yatsun hannu da kamannin fuskoki ta tantance mutane ta tabbatar su ne a kan PVC din da suke gabatarwa jami’an zabe. Ganin cewa an kwatanta ta a matsayin “hadakar fasahohi” BVAS, za ta tantance duk masu zabe ta yadda ba sai an rubuta kara ko rahoto kan matsalolin da aka samu ba.
Lokacin hirar da ya yi da Arise TV Okoye y ace “Abin da INEC ta yi hadakar fasahohi ve. Na’urar da ce ake amfani da ita wajen rajistan masu zabe. A zaben Anambra da ita za’a yi amfani wajen tantance masu zabe. BVAS din da aka kai mazabar Isoko ta Kudu a majakisar jiha ranar 23 ga watan satumba na zaben cike gurbin Jihar Delta ya nuna cewa an sami ci-gaban wajen kashi 97 cikin 100.
Wadannan tsare-tsare a cewar Biometric Update, wanda ke kawo labaran cigaban fasahohin tantance mutane, sun hada da mafita ta gane jama’a lokacin rajistan zabe, kidaya da tantancewa.
Kasashe da dama a duniya, har da na Afirka na amfani da fasahohi irin na BVAS domin su tabbatar da zabe mai sahihanci. Abubuwan da aka saba amfani da su sun hada da zanen yatsun hannu, zanen tafin hannu, kwayar ido da fuska. Akwai kuma na’urorin zaben da ake iya yawo da su.
Yana da mahimmanci a san cewa amfani da fasahar Biometrics a zabe zai taimake wajen gano siffofin da suka banbanta mutane, kamar yatsu, kwayar ido, fuska, murya da ma wasu dabi’u.
Misali mai kyau na irin nasarorin da aka samu shi ne zaben gama garin da aka yi a kasar Ghana ranar 7 ga watan Disemba 2020. A wata sanarwar manema labaran da ta fitar Neorotechnology, wani kamfanin da ya shahara kan fasahohin biometric ya ce irin fasahar da aka yi amfani da shi ke nan mai suna MegaMatcher ABIS inda aka yi rajistan mutane 17,027,641 kuma tare da taimakon wannan na’ura an gano rajistan bogi guda 15, 860 wanda ya nuna cewa mutane 7,890 sun yi kokarin yin rajista sau dayawa suna amfani da sunaye daban-daban.
Wasu kasashen Afirkan da suka yi amfani da fasahar sun hada da Uganda, Angola, Burkina Faso, Cameroon, Chad, Comoros, Jamhuriyar Dimokiradiyyar Kwango, Cote d’Ivoire, Gambia Kenya, Lesotho, Liberia, Malawi, Mali, Mauritania, Morocco, Mozambique, Namibia, Rwanda, Senegal, Sierra Leone, Somaliland, Swaziland (Eswatini), Tanzania, Uganda, Zambia, Zimbabwe.
Matsalolin na’urar
Duk da cewa ana yabon na’urar da iya gano masu magudi ta hanyar yin rajista sau da yawa, akwai wadansu matsalolin da akan fuskanta wajen amfani da shi domin ba kowani salon magudi ne zai kare ba.
Lokacin wani zaben da aka yi a Uganda sai dai aka yi watsi da shi da aka yi ta fama da rashin network. Bisa bayanan rahotannin da aka samu daga Uganda, sun danganta matsalar network din da shuga Yoweri Museveni wanda ya sa aka yanke layin yanar gizo a kasar domin a hana labarai, soshiyal mediya da sakonni kafin lokacin zaben.
Haka nan kuma saboda sarkakiyar da na’urar ke da, yawancin hukumomin zaben sai sun hada da taimakon kamfanoni masu zaman kansu. Wannan yana janyo fargaba saboda jama’a na tunanin bai dace a ce wani daga waje ya sami izinin ganin bayanan su ba. Da yawa kan so su san ko me za’a yi da bayanan su.
Ba yau ne Najeriya ta fara inganta na’urorin zabenta ba hatta a zaben Anambra na wannan watan ta yi hakan. To amma, lokaci ne kadai zai nuna mana ko matakan da take dauka za su iya dakile magudin zabe.
Discussion about this post