Zargi: Wani mai amfani da shafin Tiwita na zargi wai kwakwalwar mace kan yi rauni duk lokacin da ta ke da juna biyu kuma ya kan bukaci akalla watanni 6 kafin ya koma yadda ya ke kafin ta yi cikin.
Siffar jikin mace wakilci ne na yadda ta ke tunanin jikinta da halinta da ma yadda ita kanta take tunanin kamanninta wanda ya samo asali daga halitta, tunani da kuma tasirin yanayin zamantakewar dan adam. Duk wadannan abubuwa ne da sauyin da mace kan fuskanta lokacin da ta ke da ciki kan nuna.
Domin a lokacin da jikin mace ke sauyawa wadansu daga cikin sauye-sauyen a bayyane suke irinsu girman ciki, da kiba a yayinda wasun su kuma ba kowa ne zai iya gani ba, alal misali, irin su fadadar mahaifa, ciwon baya da laulayi.
Sauran sauye-sauyen da mace kan gani sun hada da:
– Yawan zuwa yin bawali
– hajijiya
– Kumburin ciki
– Sauyi a fatar jiki
– Girman ciki
– Sauyi a farjin ta
Da sauransu
Sai dai kwanan nan mun yi kicibis da zargin cewa wai kaifin kwakwalwar mace kan yi rauni a lokacin da ta ke da ciki, kuma wannan batu ya yi ta yawo a WhatsApp. A Shafin UberFacts (@UberFacts) da ke Tiwita ne wannan zargi ya fito ranar 21 ga watan Oktoba 2021
Ire-iren sauyin da ake samu lokacin da mace ke da juna biyu
Ciki ya kan fara ne sadda kwan na mace ya hadu da maniyin namiji, sa’annan ya gungura a hade ya manna kan shi a jikin bangon mahaifar na mace domin ya fara girma. Yawancin mata ba su iya sanin dai dai lokacin da hakan kan faru amma a wasu matan kuma su kan ga jini kadan mai kama da wanda ake gani yayin da mace ke haila.
Akwai alamu da dama da ake dangantawa da juna biyu. Wadannan alamun su kan bayyana ne cikin makonnin farko na daukan ciki. Ko da shi ke ba duka alamun ne ake gani a lokaci guda ba, kuma ba lallai ne a lokacin da aka gansu su kasance alamun ciki ba, idan dai aka dauke dukkan su a tare ana iya hasashen cewa ciki ne. To sai daibisa bayanan masana kimiya ba a riga an tantance duk wani tasirin da ake zaton ciki na da shi a kan kwakwalwa ba duk abin da aka sani yanzu hasashe ne.
A yaushe kwakwalwa dan adam ke rage girma?
Tsufa yana sauya girman kwakwalwa da tsarin yanayin yadda jijiyoyin jini suke da ma yanayin fahimtar abubuwa. Lallai kwakwalwa na sauyawa yayin da mutun ke kara shekaru kuma akwai sauye-sauye kama daga kwayoyin halitta zuwa yadda suke rikida. Tasirin tsufa a kan kwakwalwa da fahimta na da yawa kuma akwai dalilai da dama. Yayin da kwakwalwa yake raguwa, musamman a bangaren da ake kira frontal cortex, wurin da ke kula da fahimta, halayya da daukar matsaya da dabi’un mutun a yanayin zamantakewa, sa’annan su ma jijiyon jinin suka fara tsufa har aka fara samun hawan jini akwai yiwuwar samun bugun zuciya wanda zai iya janyo rauni a cikin kwakwalwar.
Bisa bayanan wani rahoto, ba sabon abu ba ne a ga sauyi a kwakwalwa yayin da mutun ke kara yawan shekaru. Ita ma fatar da ke rufe kwakwalwa wanda ake kira cerebral cortex a turance ta kan rage kauri, kuma ana iya ganin hakan a bangaren da ake kira frontal lobe, wurin da ke ajiye abubuwan da akan tuna, abubuwan sosa rai, dabarar shawo kan matsaloli, cudanya da jama’a da kuma ayyukan motsa jiki. Ana kuma iya ganin wannan raguwar kaurin a temporal lobe wanda ke bayan kunnuwa, wanda shi ne ke taimakawa dan adam wajen gane kalmomi, magana, karatu, rubuta da ma hada kalmomi ta yadda za su yi ma’ana.
Bangarorin kwakwalwar da ke raguwa suna da jijiyoyi wadanda ke kama da bututu. Bututun ne ke kai bayanai daga kwakwalwa zuwa bangarori daban-daban na jikin dan adam, sa’annan su sake daukar wasu bayanan da bangarorin jikin mutun su kai kwakwalwa. Yayin da dan adam ke kara shekaru, irin wannan ma’amala tsakanin jiki da kwakwalwa kan ragu abin da ka iya janyo matsaloli da dama.
Bisa la’akari da irin wadannan bayanai, za’a iya cewa kwakwalwar mace mai juna biyu na raguwa?
Tantancewa
Shugaban sashen kula da mata masu juna biyu da asibitin uwa da yara na jihar Ondo Dr Ayodele Adewole ya ce hakan ba gaskiya ba ne “Babu gaskiya ko kadan a wannan batu, ba abin ya yi nisa da gaskiya kamar haka, karyace kawai aka shirga. Kwakwalwar mai juna biyu ba ta raguwa, tsufa ce kawai ke rage kwakwalwa kuma ba abin da ya hada juna biyu da kwakwalwa.”
A waje guda kuma, babban darektan likitoci na asibitin koyarwa a jami’ar kimiyyar lafiya (UNIMED) Dr Adesina Akintan ya ce kimiyya ba ta riga ta sami hujjojin da suka nuna haka ba.
“Ban san wannan zargi na cewa kwakwalwar mace kan ragu yayin da take da juna biyu, sa’anna wai yana bukatar watanni 6 kafin ya koma yadda ya ke ba, babu hujjojin kimiya da su ka tabbatar da wannan dan haka ni ban yadda ba, babu wani tushen kimiyya da zan iya kamawa dangane da wannan batun,” ya ce.
Wani binciken da aka wallafa a wata kasidar kimiyyar kwakwalwa ya ce akwai sauye-sauyen da kan afku a kwakwalwar mace yayin da ta ke da juna biyu. Binciken ya ce kwakwalwan kan ragu amma kaifin shi kan karu, domin a cewar binciken wannan sauyin na shirya mace ne ta yadda za ta tinkari kalubalen da ke zuwa da zama uwa.
Sai dai wani binciken kuma ya sake bayyana cewa yanayin kwakwalwar mace kan sauya baki daya sadda ta dauki cikin farko, kuma wadannan sauye-suayen za su kai tsawon shekaru 2. Wata kila wannan na nufin kwakwalwar kan sauya a fanninin da zai taimaka mu su misali wajen lakantar ire-iren bukatun jarirai ko kuma gano irin barazanar da kananan yara ka iya fiskanta. Ya kuma kara da cewa raguwar sinadarin grey matter, wato wani ruwan da ake samu a kwakwalwa ba lallai ne ya kasance abu mara amfani ba, zai iya yiwuwa alama ce ta dattijantaka ko kuma kwarewa.
A Karshe
Duk da cewa akwai binciken da ke fitowa dangane da wannan zargi babu hujjojin da ke bayar da tabbacin cewa kwakwalwar mace na rage kaifi a lokacin da take dauke da juna biyu har ma yana bukatar watanni shidda kafin ya koma yadda yake a baya.
Discussion about this post