‘Yan bindiga sun kashe limamain masallacin Sabon Garin Bilbis Malam Adam a gonar sa.
Majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa ‘yan bindigan sun iske liman malam Adamu a gonar sa ne yana aiki tare da wasu mata.
Sun tilasta shi ya bi su, wai sun yi garkuwa da shi, liman Adamu ya ce kafar sa ke ciwo ba zai iya bin su cikin kungurmin daji ba saboda haka su yi hakuri su kama gaban su kawai.
Daga nan ne wani ya yi barazanar kashe da bindiga, liman kuma ya tirje ya ce ba zai bi su ba. Shi kenan sai daya daga cikin su ya harbe shi, na take ya fadi mutacce.
Bayan haka sai suka yi awon gaba da sauran matan dake aiki a gonar liman din.
Wasu maharan da ban kuma sun saki mutum 25 da suka yi garkuwa da su a acikin makon jiya. Cikin wadanda aka sace har da yayan wani mazauni biyu.