Alkaluman sakamakon binciken gwajin cutar korona da hukumar dakile yaduwar cututtuka ta ƙasa NCDC ta fitar na ranar Lahadi ya nuna cewa cutar ta yi ajalin mutum 26 a kasar nan.
Hukumar ta Kuma ce a wannan rana mutum 165 ne suka kamu da cutar.
Bayan haka NCDC ta ce ta hada mutum 23 da cutar ta kashe a jihar Legas daga ranar 18 zuwa 20 a cikin adadin yawan mutanen da cutar ta kashe.
Akwai kuma mutum 3 da suka mutu da aka hada a ciki da aka samu daga Abuja ranar 23 ga Oktoba.
Daga nan kuma akwai mutum 77 da suka kamu da cutar daga ranar 21 zuwa 24 a jihar Legas sannan da mutum 43 da suka kamu ranar 23 a Abuja da aka hada a cikin jimlar yawan mutanen da suka kamu da cutar.
Zuwa yanzu mutum 210,460 ne suka kamu da cutar sannan an sallami mutum 202,379 a kasar nan.
Yaduwar cutar
Legas – 77,676, Abuja-23,117, Rivers-12,607, Kaduna-10,009, Filato-9,644, Oyo-8,742, Edo-6,568, Ogun-5,371, Kano-4,328, Akwa-ibom-4,338, Ondo-4,545, Kwara-3,930, Delta-3,514, Osun-2,985, Enugu-2,675, Nasarawa-2,462, Gombe-2,566, Katsina-2,212, Ebonyi-2,048, Anambra-2,346, Abia-1,975, Imo-1,973, Bauchi-1,667, Ekiti-1,742, Benue-1,679, Barno-1,344, Adamawa-1,136, Taraba-1,074, Bayelsa-1,232, Niger-1,056, Sokoto-796, Jigawa-587, Yobe-501, Cross-Rivers-625, Kebbi-458, Zamfara-276, da Kogi-5.
Gwamnatin jihar Kaduna ta gargaɗi ma’aikatan jihar da mutane kowa ya garzaya a yi masa rigakafin korona sannan a bashi shaidar yi domin nan da kwanaki 10 idan ba ka da shi ba za aka shiga ofisoshin gwamnatin jihar ba.
Gwamnati ta ce ranar Asabar ce ranar ƙarshe da za yadda wa ma’aikaci ko bakon ofisoshin gwamnatin jihar ya shiga ba tare da ya nuna shaidar yin rigakafin cutar ba.
Kwamishinar kiwon lafiya, Amina Baloni ta hori ƴan jihar su garzaya cibiyoyin kiwon lafiya dake kusa da su domin yin rajista.
Dokar dai zai fara aiki ne daga ranar 31 ga Oktoba.
Discussion about this post