Akalla mutum 47 ne mahara suka kashe a kasar nan a makon da ya gabata.
Daga cikin mutum 47 din da aka kashe akwai sarakunan gargajiya biyu, soja daya sannan da mutane.
Jihar Sokoto
A kasuwar Goronyo dake jihar Sokoto ‘yan bindiga sun kashe mutum 43.
Maharan sun dauki akalla awa biyu suna zubar da jinin mutane a kasuwan ba tare da jami’an tsaro sun kawo dauki ba.
Jami’an tsaro sun ce mutum 43 ne aka kashe a harin kasuwan Goronyo amma mutane sun ce mutum 62 be aka kashe.
An kashe sarakunan gargajiya biyu a jihar Imo
A ranar Talata ne wasu ‘yan bindiga sun buda wa taron sarakunan gargajiya wuta inda biyu suka mutu sannan da dama sun ji rauni.
An kashe dan sanda daya a jihar Kwara
Rundunar ‘yan sanda a jihar Kwara tabayyana cewa ‘yan bindiga sun kashe daya daga cikin ma’aikatanta Sina Babarinde dake aiki a Ilorin.
Kakakin rundunar Okasanmi Ajayi wanda ya tabbatar da haka ranar Litini ya ce ‘yan bindigan sun kashe Babarinde ranar Lahadia cocin ‘Christian Church of God (RCCG), Living Word Parish’ dake hanyar Basin a Ilorin.
An kashe soja daya a jihar Imo
Discussion about this post