Kasurgumin Dan Bindiga mai suna Damina wanda ya abbabi yankin Dansadau dake Karamar Hukumar Maru, a Jihar Zamfara ya gamu da ajalinsa a makon jiya.
Da farko dai Damina ya ji rauni ne sakamakon harbin bindiga daga wani bangaren Yan bindigan daga yaran wani gogarman, Dogo Gide, a arangama da aka yi a yankin garuruwan Chilin da Fan-Maje a dajin Kwiambana dake a yankin na Dansadau.
Dama a baya Dogo Gide yana neman Damina ruwa a jallo tun a baya sabani ya shiga tsakanin su wajen rabon kayan sata da kuma rikicin iko da yanki.
Ana cikin rikicin ne Damina ya shiga garin Babban Doka inda Dogo Gide yake da iko da ya kashe mutum goma ciki har da kananan Yara.
Damina ya kuma sa wa Yan garin na Babban Doka dokar dole su tara masa kudi har miliyan shida wanda kuma aka tara masa amma a wajen amsar kudin yaran Dogo Gide suka yi masa kwantar bwana.
Damina ya sami rauni sakamakon harbin bindiga inda ya gudu garin Farin Ruwa yana jinya a gidan wani mai suna Mua’azu Dallali.
Daga bisane yaran Dogo Gide suka bishi har can garin na Farin Ruwa inda yake jinya suka yi masa gunduwa-gunduwa suka cire masa kai da kafafuwar sa.
Sun kawo kan Damina da kafafuwarsa garin Babban Doka inda Yan garin da shi Damina ya abdaba suka yi ta yin murna suna shagali.
Dama Dogo Gide yayi alkawarin bada lada ga duk yaron sa da ya kashe masa Damina.
Discussion about this post