Jihar Kaduna na daga cikin jihohin Arewa da masu sharhin siyasa ke yawan yin tsokaci akan makomar ta musamman ganin yadda zaɓen 2023 ke daɗa tunkarowa.
Saura watanni biyu kacal ayi sallama da 2021, a shiga 2022, wato shekarar da za fidda ƴan takara za a yi zaɓukan fidda gwanaye da dai sauran tashi faɗin siysa.
Malam Nasir El-Rufai ya zama ƙarfen kafa a jihar Kaduna, tun bayan ɗarewarsa kujerar gwamna a 2015, ya fara canja fasalin siyasar Kaduna.
Wasu daga cikin waɗanda ake ganin idan suka ce ca, ba a isa ace kule ba a siyasar Kaduna, sai gashi sun zama karan naɗa miya kamar almara.
Wasu da dama an ɗauko tafiyar da su amma tuni ta ɓare da su, aka karkata akalar tafiyar ba su.
Sanata Shehu Sani shine mutum na farko da ta fara tuntsirewa da shi, ba ayi ko shekara daya da fara gwamnatin APC a jihar Kaduna ba, kowa ya kama gabar sa tsakanin sanatan da gwamna El-Rufai. Hakan ya sa a karshe dai dole ya fice daga APC ya koma PRP domin sake yin takarar kujerar sanata. APC ta musanya Shehu Sani da babban Aminin gwamna El-Rufai, wato Uba Sani, akarshe dai Uba Sani ne ya yi nasara a zaben a 2019.
Da ga shi sai kuma Sule Hunkuyi wanda ake ganin shine mukullin siyasar Kaduna, idan kayi da shi ta fishe ka idan ka ki ka kwan ciki. Shi ma bai tsira daga laujen Malam ba domin ta wafce shi da yasa dole ya tattara nasa-ina sa ya koma jam’iyyar PDP domin takarar gwamna jihar a 2019. Sai da a can ma bai sha da daɗi ba domin tun a zaben fidda gwani Isah Ashiru yayi wasan kura da shi, ya yi mai kifa ɗaya kwala, bashi ga tsuntsu ba shi ga tarko.
Tafiya ta yi nisa wasu an taho da su a tafiyar daga farkon 2019, sai dai kash, tun kafin ta yi nisa ta kife da su, aka fara takun saƙa tsakanin gwamna da su. Ɗaya daga cikin su kuwa shine Aminu Shagali, Kakakin Majalisar jihar, majalisar jihar ta tsige shi ta masanya shi da Yusuf Zailani wanda yanzu shine ɗan gaban goshin gwamna El-Rufai, kamar yadda masu fashin baƙi a siyasar Kaduna suka faɗi.
A majalisar akwai irin su Haruna Mabo, shima dai yanzu ba a san madafar sa a siyasar Kaduna ba, domin ba da dadewa ba majalisar jihar ta tsige shi daga kujerar shugaban masu rinjaye na majalisar jihar Kaduna.
Shima ɗan majalisar tarayya Samaila Suleiman ya yi shiru, wasu daga ɓangaren sa sun bayyana cewa tuni ya kama gaban sa, ba ruwan sa da tafiyar Malam, bai dai bayyana ficewa daga APC ba har yanzu.
Ana hasashen cewa akwai yiwuwar gwamnan Kaduna El-Rufai ya goyi bayan matashi ne a 2023, sai dai ba a san wanne ne cikin matasan dake kewaye da shi zai marawa baya ba.
Haka kuma wasu na ganin hakan zai kawo wawukeken ɓaraka a jam’iyyar domin akwai jigajigan ƴan siyasa dake ganin da su aka kafa APC a jihar sannan suka yi mata bauta suna ganin sune suka cancanci kujerar gwamnan jihar idan Malam ya karkare wa’adin mulkin sa a 2023.
Yanzu dai kowa na wasa wuƙar sa ne, ba a APCn ba ba a PDP ba.
Ko irin dimbin ayyukan da gwamna El-Rufai ya kantara a jihar Kaduna wanda ba a taba ganin irin su ba zai yi masa tasiri a 2023, wato ya tsaida ɗan takara jama’ a su kuma yi masa biyayya?
El-Rufai zakaran gwajin dafi ne a jihar Kaduna, domin babu fannin da bai canja fasalinsa ba, ya zama irin na zamani, birnin Kaduna da wasu manyan birane a jihar, Zariya da Kafanchan sun ɗanɗana ayyukan cigaba da El-Rufai ya ke yi.
Toh za ace Allah ya maimaita mana ne ko …?
Wasu daga cikin waɗanda ake wa hasashen ɗayan su zai iya samun goyon bayan gwamna El-Rufai sun haɗa da Malam Uba Sani, Mohammed Abdullahi, Hafiz Bello, Mataimakiyar sa Hadiza Balarabe, Kwamishinan Tsaro, Samuel Aruwan, Kakakin majalisar Jihar Yusuf Zailani da dai sauran su.
Discussion about this post