Boko Haram ɓangaren ISWAP sun kai wa sansani sojoji dake Katarko, ƙaramar hukumar Gujba, Jihar Yobe ranar Asabar.
Majiya daga ɓangaren Sojoji da mutanen wanna ƙauye sun ce Boko Haram sun afka wa barikin Sojojin ne inda suka yi artabun barin wuta a tsakanin su. Hakan ya sa mutane arcewa cikin daji a lokacin da ake batakashin.
Tsakanin kauyen Katarko da babban birnin jihar Yobe, Damaturu, bai wuce tafiyar kilomita 20 ba. Kauyen yayi fama da hare-haren Boko Haram.
Majiya ta shaida cewa Boko Haram sun zo sansanin sojojin a cikin motocin yaki 10, sannan bayan arangamar da suka yi Ƴan ta’addan sun kwashi akwatinan bindigogi da makamai.
Wani mazaunin kauyen Katarko, Modu Aji ya ce yana gonar sa ya ji rugugin harbi. Matafiya da dama dole suka tsaida tafiyarsu cak.
Matafiya sun yi cincirindo a titin, duna jiran Sojoji su basu damar wucewa.
Discussion about this post