Jam’iyyar PDP ta damka wa shiyyar Arewa su fito da shugaban Jam’iyyar.
Hakan ya biyo bayan taron da kwamitin gudanarwar jam’iyyar ta yi ranar Alhamis a Abuja.
Shugaban kwamitin rarraba mukamai na jam’iyyar, gwamna Ifeanyi Ugwuanyi ya ce idan zaɓen shugabancin jam’iyyar ya zo, Yankin Arewa ce aka damƙa wa fidda shugaban jam’iyyar.
Wannan matsayi ya dagula wa masu zamman yin takarar shugaban kasa a a jam’iyyar daga Arewacin Najeriya.
Kamar yadda jam’iyyar ta saba, idan shugaba ya fito daga yankin kudu toh, shugabancin kasa zai koma Arewa ne, idan kuma daga Arewa ne, takarar shugabancin kasa zai koma kudu kenan. Yanzu dai ya nuna kudu PDP ta karkata.
Discussion about this post