Duk da cewa Gwamnatin Tarayya ta ɗauko hanyar kawar da bambaci tsakanin mai takardar shaida kammala Digiri (BSc) da mai Babbar Difiloma (HND), za a ci gaba da nuna wannan bambancin fifito wajen ɗaukar aiki, har sai bayan an kammala gyaran tsarin aikin ɗaukar ma’aikata tukunna.
Haka dai wani babban jami’in gwamnatin tarayya ya bayyana a ranar Laraba.
Yayin da ake ganin mai digiri na farko da mai HND duk kusan ɗaya su ke, sai dai kuma a wajen ɗauka aiki ana fifita mai digiri a kan mai HND.
‘Yan Najeriya da dama, ciki har da Ƙungiyar Malaman Manyan Kwalejojin Fasaha (ASUP), sun daɗe su na kiraye-kirayen gwamnatin tarayya ta cire wannan nuna fifiko da ake yi.
A ranar Laraba dai Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Folasade Yemi-Esan ta jaddada ƙoƙarin da gwamnatin tarayya ke yi don ganin an cire wannan bambanci.
Sai dai kuma ta ce a yanzu hakan ba zai yiwu ba, har sai an kammala aikin gyaran tsarin ɗaukar ma’aikata wanda a yanzu ake kan aiwatarwa tukunna.
Haka Yemisi ta shaida wa manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa, jim kaɗan bayan kammala taron Majalisar Zartaswa tare da Shugaba Muhammadu Buhari, a ranar Laraba.
Discussion about this post