Shugaba Muhammadu Buhari wanda kuma shi ne Ministan Man Fetur, ya bayyana cewa kamfanin NNPC ya samu riba ta naira biliyan 287, zunzurutu bayan an ware kuɗaɗen haraji, a cikin 2020.
Shugaba Buhari ya yi bayanin a cikin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labarai Femi Adesina ya sa wa hannu, kuma ya fitar da sunan shugaban ƙasar.
Buhari ya ce bayyana sakamakon ribar cika alƙawari ne da gwamnatin tarayya ta yi cewa za ta bayyana adadin ciniki da ribar da ta samu a NNPC.
Buhari ya ce wanann riba ita ce ta farko a cikin shekaru 44 da aka kafa NNPC.
“Ina farin cikin bayyana cewa NNPC ya samu riba har ta naira biliyan 287 bayan an biya kuɗin haraji a cikin yawan ribar, a shekarar 2020.
“NNPC ya rage tafka asara daga naira biliyan 803 da ya ɗibga cikin 2018 zuwa naira biliyan 1.7 a cikin 2019.
“A shekarar 2020 kuwa riba ya samu maimakon faduwar da ya shekara 44 ya na tafka asara a tsawon tarihin kafuwar sa.
“Wannan nasara kuwa ta samu ne saboda taka-tsantsan da kuma bin ƙa’idar ririta kuɗaɗen ƙasar nan da wannan gwamnati ke yi, domin amfanar al’umma baki ɗaya.”
Buhari ya gode wa Hukumar Gudanarwar NNPC da ɗaukacin ma’aikatan NNPC tare da fatan wannan riba da aka samu za a ɗore a haka.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga cewa Buuhari zai bayyana adadin kuɗaɗen cinikin fetur na 2019 da 2020.
Shugaban Kamfanin NNPC Mele Kyari, ya bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari zai yi bayanin cinikin fetur da ƙididdigar shekarun 2019 da na 2020.
Kyari ya yi wannan bayanin ga Kwamitin Majalisar Tarayya Mai Sa-ido Kan Harkokin Kuɗaɗe a ranar Laraba a Abuja.
Shugaban na NNPC ya bayyana a gaban kwamitin domin gabatar da bayanan hasashen irin kuɗin shigar da NNPC za ta samu shekarar 2022-2024.
Ya yi ƙarin hasken cewa sakamakon da Shugaba Buhari zai bayyana, abu ne da jama’a za su yi farin ciki da shi.
Wannan albishir da Kyari ya yi wa mambobin kwamitin dai ya sa zukatan ‘yan kwamitin sun yi murna tare da taɓa masa.
A tarihin NNPC dai ba ta bayyana ciniki da ribar da ta samu a kowace shekara. Sai da cikin shekarar da ta gabata da ta fara shi, tun shekaru 43 da su ka shuɗe ba ta yi ba, sai cikin 2020.
“Shugaban Kwamiti, ina sanar da kai da sauran ‘yan kwamiti cewa ba yanzu ya kamata na yi bayanin kuɗaɗen shigar da NNPC ta samu ba. Shugaban Ƙasa ne da kan sa zai yi wannan bayani.
“Ina tabbatar maka muna da ƙididdigar kuɗaɗen shiga na 2019 da na 2020 ajiye tsaf, a kammale. Kuma za a yi alheri daga bakin Shugaban Ƙasa.” Inji Kyari.
A bayanij sa, Shugaban Kwamitin Majalisar Tarayya Mai Sa-ido Kan Harkokin Kuɗaɗe, James Faleke, ya ce wa Kyari, “Yanzu dai kuma tara riba mai yawa. Yau dai ka burge mu.”
Kyari ya ci gaba da cewa nan gaba kaɗan Najeriya za ta daina shigo da tataccen man fetur, ta riƙa fitar da tataccen zuwa ƙasashen waje.
Daga nan kuma ya kare aniyar Gwamnatin Tarayya ta zuba jari ko mallakar kashi 20% bisa 100% na Matatar Ɗangote. Ya ce an yi haka ne domin a riƙa tilasta wa Ɗangote sayen ɗanyen mai na Najeriya ya na tacewa a sabuwar matatar sa da za ta fara aiki nan ba da daɗewa ba.