Masu Gidan Rana, Daga Muazu Muazu

0

Kashi 98 cikin dari na rayuwar kowanne mutum a wannan duniya ta dogara ne akan kudi. Ko da kuwa an san hakan ko ba a sani ba.

Kuma rayuwar duniya in babu kudin, to babu abin da ake kira jin dadi.

Kuma sau da yawa idan abu ya lalace, in aka tarfa masa kudi sai ya gyaru.

Ita dukiya kamar sauran abubuwan dake kewaye da mu ne a wannan duniya, tana da matukar muhimmanci, kuma muhimmancin ta ne ma ya sa kowa yake neman ta. Talaka da basarake, mai mulki da wanda ake mulka, namiji da mace, babba da yaro, kai har wanda ba shi da hankali ma. Na ga wata mai ta6in hankali a unguwarmu, in ta ga mutum zai wuce sai ta shiga gabansa ta ce masa “Ban biyar”. Ka ga wanda bai da hankali ma kenan.

Duk wanda ya yi wa kudi bauta tsawon shekaru 20, to su kuma za su yi masa bauta har abada.

Masana da dama sun yi rubuce-rubuce akan neman kudi da sarrafa su, haka ma malamai sun yi maganganu da dama akan falalar dukiya da alherinta

Kuma Manzon Allah Ya ce, a samu mutumin kirki yana da dukiya mai yawan gaske kuma mai taimakon mutane.

Duk wanda ya samu ikon ya zama babu kamar sa a kudi ko dukiya, to ya zama babu laifi, saboda in sarrafa ta ta hanyar mai kyau, to zai dace, kamar yadda Dr Mamman Shata yake cewa a cikin wata wakarsa “Kudi a kashe su ta hanya mai kyau” “In kai aiki ka samu kudinka, to ka kashe su ta hanya mai kyau”

Ni ma mai rubutu burina a ce ina da miliyoyin fam din kasar Ingila ko dalar Amurika, ko nairar kasata Nigeria. Na yi alheri kuma na kashe su ta hanya mai kyau.

Babban abin da ke damun mutane yanzu shi ne, rashin ilimin abin da ake kira (financial management), wato hanyar da za a tafiyar da kudin a sarrafa su in an same su, da ma yadda za ka juya su har ka iya rike su. Wannan Ita ce matsalar.

Kudi abin nema ne kamar Shata ya fada, kuma duk iliminka bai zai sauka daga wannan magana ba, hasalima in ka sauka daga kan ta za a iya cewa ka samu matsala a tunaninka.

Sahabban Manzon Allah, tun daga lokacin da ya je Haidar har shekara dari babu talaka a cikin su.

Babu wanda ko dan sa ya zama talaka.

Annabi kansa ba talaka ba ne. In ka ji an ce ana kwanaki ba a dora tukunya a gidansa ba, ba don babu ne, saboda kyauta ne kawai irin ta Manzon Allah (S.A.W).

Wata matsalar kuma da muke da Ita, ita ce ba mu iya neman kudi ba, shi ya sa muka kasa fita daga cikin rashin kudi (talauci).

Lallai mutane du tashi su neman ilimin yadda ake neman kudi da kashe su.

Idan ka zama talaka a yau, to kasarwarka ce ta ja maka ba wani ba.

Ba laifi ba ne don iyayen da suka haife ka, sun zama talakaw, amma kai yi kokari ka zare jikinka daga talaucin har ka taimaka musu.

Sannan kar mu manta amana tana da muhimmanci a neman kudi. Ka zama mai rikon amana.

Kudi ba abin da ya fi su tasiri a rayuwa in ka cire ilimi, kuma ba a fi su biyayya ba, ba a fi su kirki ba, ba a fi su nagarta ba, sannan ba a fi su tausayi ba.

Sai dai tare da haka babu abin da ya fi su lalata. Ko dan adam bai fi kudi lalata ba.

Duk wanda ya ce maka ka fiye son kudi, to raina ka ya yi, haka wannan magana take ba ko musu, domin kowa na son su, har da wanda ya fada maka hakan.

Don haka a tashi a nemi kudi, amma ban da na haram, kuma a yi zakka, domin ba ta cinye dukiya, karawa ma take yi. Kuma a yi alheri da su, don sun fi son a yi alheri da su.

An kashe su ta hanya mai kyau kenan.

Share.

game da Author