Kotu a Mararaba dake jihar Nasarawa ta yanke wa wata Uwa mai suna Onyenye da’yarta Gift Omoyo hukuncin zama a kurkuku na tsawon watanni uku saboda dambe da suka saba yi kullum a tsakanin su.
Alkalin kotun Abubakar Tijjani ya ba matan zabi, ko su biya naira 5,000 kowannen su ko kuma zaman kurkuku na wata uku, saboda tada hankalin jama’an unguwa da suka yi.
Dan sandan da ya shigar da karar saja Hamen Donald ya bayyana cewa a ranar 15 ga Juni Onyenye ta kawo kara a ofishinsu dake Mararaba cewa ‘yar ta Gift ta lakada mata dukan tsiya har ta jijji mata rauni a jiki.
Donald ya ce sai dai binciken da suka gudanar ya nuna cewa Onyenye da Gift makwabtan juna ne sannan a wannan rana sun yi dambe tsakaninsa ma zafi.
Ya ce sun yi wa juna jina-jina a jiki.
A zaman da kotun ta yi Oyenye da Gift sun amsa laifin da suka aikata sannan sun nemi sassauci daga wajen alkalin.
Discussion about this post