Soja ya bindige budurwarsa a dalilin zargin tana yi masa yankan baya

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Bayelsa ta bayyana cewa ta tsinci gawar wata yarin mai suna Jennifer Ugadu mai shekaru 23 a dakin ta bayan wani saurayinta soja ya harbe ta da bindiga.

Kakakin rundunar Asinim Butswat ya sanar da haka a wata takarda da aka raba wa manema labarai a garin Uyo a cikin wannan makon.

Butswat ya ce sun tsinci gawar Jenifer ranar 13 ga Yuli bayan sanar da rundunar da wata kawar marigayiya Jennifer ta kawo ofishin yan sanda.

“Kawar ta bayyana cewa saurayin ya rubuta a kafar sada zumunta a yanar gizo wato Whatsapp cewa shi ya kashe Jennifer kuma shima zai kashe kansa saboda abinda ya aikata.

Butswat ya ce sakamakon binciken da suka gudanar ya nuna cewa saurayin Jennifer soja ne mai suna James Matol sannan ita Jennifer dalibar jami’ar Neja-Delta ne dake Bayelsa.

Ya ce James ya kashe Jennifer saboda zargin yi masa yankan baya da take yi da wasu samarin, da ko ya fusata sai ya dirka mata bindiga kawai

Bayan haka a ranar Alhamis kakakin rundunar sojin Najeriya Onyema Nwachukwu ya bayyana cewa rundunar za ta gudanar da bincike akan abin da ya faru.

Nwachukwu ya ce rundunar za ta ci gaba da kare hakin mutanen Najeriya bisa ga tsarin dokokin kasar kuma lallai rundunar za ta hukunta James kan laifin da ya aikata.

Share.

game da Author