HIMMA DAI MATA MANOMA: Yadda makiyaya su ka banka shanu su ka cinye min gonar Kabushi da Kabewa ƙarƙaf a gaba na – Manomiya Naomi Yusuf

0

A Toto da ke Jihar Nassarawa, akwai wata mace mai himmar noma da ake kira Naomi Yusuf. Ba ta yi ƙarfi a harkar noma ba, amma akwai ta da ƙwazo sosai.

Naomi ta na noman masara, gurji ko kankana da kuma gyaɗa. Zuwa yanzu ta shafe shekara 30 kenan ta na noma.

“Ni asalin ‘yar Jihar Kogi ce. A can ban taɓa yin noma ba. Zaman aure ba ke yi, amma ina sana’ar sari itacen girki a jeji, kuma ina yin aikatau a gidaje ana biya na. Idan na samu wani aikin ƙarfi a cikin gungun mata ‘yan ina-da-aiki, na kan shiga na yi.

“Farkon zuwa na Toto, ina bin matan-ƙauye mu na zuwa ƙwadago a gonaki. Wata rana sai wata mace ta ce min, me zai hana ni ma na yi nawa noman? Da na yi mata kukan rashin gona, sai ta ɗan ɗibar mani wuri a cikin gonar ta. To daga baya sai ta mutu.

“Tun ana ba ni aron ɗan wuri na noma, har aka daina. Saboda ni dai ba biyan ladar aro na ke yi ba. A gefe ɗaya kuma akwai mutanen da ke karɓar aron gona su biya su yi noma a cikin ta.

“A yanzu dai ina da hekta biyu. Ita ɗin ma wani mutum na samu ya karɓo min aron ta. Don idan da kai na na je don a ba ni aron gonar, to sai an cuce ni, an tsawwala min kuɗi.”

Naomi ta bai wa wakilin mu labarin yadda wasu gungun makiyaya su ka tura shanun su su ka cinye mata gurji da kankana ƙarƙaf a gaban ta, ta na tsaye ya na kallo.

“Wata rana da cikin watan Mayu na wannan shekarar, ina cikin gona sai wasu Fulani makiyaya su biyar su ka danno cikin gona ta da shanun su masu yawa.

“Amfanin gona ta duk sun ƙosa ina tunanin fara cirewa. Kawai sai su ka danno shanun su, su na ci min amfanin gona.

“Da na fara ihu, ina kururuwar neman taimako daga jama’a, sai su ka yi na rufe baki, na cika raki.”

Naomi ta ce shanun su ka cinye dukkan amfanin gonar ƙarƙaf. Su ka ce wai gonar su ce, kuma manoma sun dame su, duk wani manomi ya zauna gida, ya daina fita noma.

“Na ce masu ni talaka ce, abinci na ke nema. Su ka ce babu ruwan su, wannan matsala ta ce, ba ta su ba. Ko cikin makon da ya wuce masu garkuwa sun arce da wasu manoma daga gonakin su. Shi ya sa mata da maza da yawa sun daina zuwa gona, kada a yi biyu babu, babu mai gona kuma ba gonar.”

Naomi ta ce ba ta samun irin shukawa a hannun gwamnati. “A kasuwa na ke saye. Kuma na kasuwa ba shi da nagari sosai.

“Haka taki kuwa ina samu a ƙaramar hukuma na saya. Kuma ina saye a kasuwa. Sai dai maganar gaskiya takin ya yi tsada sosai.”

Naomi ta ce a kasuwar Toto ta ke sayar da duk abin da ta noma. Kuma saboda a yanzu an san ta sosai, ta kan sayar da komai, ba ya kwantai. Har da rubabi-rubabin sayarwa ta ke yi.

A ƙarshe ta ce duk da shekarun ta sun ja sosai, ba ta kai ƙarfin ɗaukar ma’aikata ta na biyan su a yi mata noma ba. Amma dai ‘ya’yan ta kan taya ta, a duk lokacin da su ke da sararin zuwa su taimaka mata da noman.

Ta ce ba ta taɓa samun wani tallafin noma daga gwamnati ko wata ƙungiya ba.

Babban ƙalubalen da ta ce ta na fuskanta, shi ne rashin kuɗi da rashin ƙarfin iya sayen kayan dabarun noma da kuma rashin tsaro.

“Idan ba ka da ƙarfin sayen kayan noma na zamani, ba za ka taɓa inganta harkokin noman ka ba. Ina kira gwamnati ta shigo ta tallafa mana da kayan aiki. Kuma ta magance mana matsalar tsaro.”

Share.

game da Author