Abba Kyari ya ja na shi Dalolin daga wurina – In ji ‘Hushpuppi’ a kotun Amurka

0

Tantirin ɗan damfara da ke fuskantar tuhuma a kotun Amurka Hushpuppi ya bayyana wa Kotu a Amurka cewa fitaccen ɗan sandan Najeriya da yayi suna wajen kamo barayi da ƴan bindiga, Abba Kyari na daga cikin waɗanda suka karɓi kuɗade daga hannun sa cikin kuɗaden damfara da ya rika yi wa mutane a baya.

Hushpuppi na fuskantar tuhuma a kotun Amurka inda ya amsa laifin aikata damfara sannan ya bayyana sunan Abba Kyari cikin waɗanda suka amfana da waɗannan kudade.

Hushpuppi ya ce ya rika saka Abba Kyari yana kama masa abokanan harkallarsa a Najeriya musamman waɗanda ba su jituwa, sannan ya na aika masa da kuɗaɗe daga cikin kuɗaden damfarar da yanzu ake tuhumar sa akai a Amurka.

Sai dai kuma Abba Kyari ya karyata hakan a shafinsa ta Facebook inda ya ce babu abinda ya haɗa shi da Hushpuppi da ya kai sun yi musayar kudi a tsakanin su.

” Abinda na sani shine na taɓa haɗashi da wani Tela yayi mashi ɗinki kuma ya biya shi naira 300,000, kuɗin ɗinkin.

Hushpuppi ya yi kaurin suna a Dubai inda ya ke da zama, ta yadda yadda ya rika dakasharama, tabargaza da ragargazar kudade.

Ya rika tafiyar da rayuwar sa wajen sayen komai Mai tsadar gaske a duniya, tare da rika bayyana dukiyoyin da ya mallaka a soshiyal midiya.

“…ku da ke ta surutan banza a kai na, kamata ya yi ku yi amfani da labari na domin ku ba marasa galuhu kwarin-guiwar samun kyakkyawar madogara.” Inji Hushpuppi cikin wani bidiyo.

“Amma sai surutai ku ke ta yi ku na jin cewa al’umma ba za su yi gam-da-katar a rayuwa ba. Ku a tunanin ku kawai zama cikin kuncin rayuwar talauci ce ta dace da ni.”

Share.

game da Author