Manyan garuruwan ƙasar nan ciki har da Legas da Abuja sun kwana cikin duhu a ranar Laraba sakamakon durƙushewar da babbar tashar daga wutar lantarki ta yi.
Kamfanonin Sayar da Wuta ne su ka bayyana labarin durƙushewar, wadda ita ce ta huɗu a cikin wannan shekara.
Rashin wutar ya shafi garuruwa da dama, wasu ma tun a ranar Lahadi wasu kuma a ranar Laraba.
Kamfanin Raba Wuta na Eko Electricity Distribution Company da ke Legas ya ce “Mu na bada haƙuri saboda rashin wutar da ake fama, ya samo asali ne daga durƙushewar tashoshin bada wuta. Amma mu na aiki tare da Hukumar Saida Wuta TCN, domin a ga an saidaita matsalar.”
Shi ma Kamfanin Raba Wuta na Ikeja da ke Legas, ya yi irin wannan sanarwa. Shi ma na Abuja (AEDC), ya yi irin wannan sanarwa ta hannun Jami’in Hulɗa da Jama’a na AEDC, Oyebode Fadipe, ya ce babbar tashar wutar lantarkin ta durkushe wajen ƙarfe 12: 26 na ranar Laraba.
Sanarwar ta ce jihohin da abin ya fi shafa, su ne masu kusanci ko Babban Birnin Tarayya, Abuja.
“Mun kasa samar da wuta a jihohin Kogi, Nasarawa, da Neja da kuma kusan gaba ɗaya ƙwaryar birnin Abuja.”
“Zuwa yanzu da na ke maka magana, migawat 20 kaɗai Abuja ta samu, maimakon migawats 400 da aka saba turowa a Abuja ɗin.”
Sauran biranen da abin ya shafa har da Egugu da Fatakwal da wasu garuruwa da dama.
Discussion about this post