Gwamnatin jihar Bauchi ta fara kidayar karuwai dake zama a jihar.
Shugaban hukumar Hisba na jihar Aminu Balarabe ya sanar da haka a taron da aka shirya domin haka ranar Laraba a garin Bauchi kamar yadda kamfanin dillancin Labarai ta ruwaito.
Balarabe ya ce gwamnati ta yi haka ne domin gyara rayuwan karuwan ta yanyar horas da su sana’o’in hannu da basu jari domin hana su ci gaba da karuwanci a jihar.
Ya ce gwamnati za ta maida karuwan dake so wadanda ba ‘yan asalin jihar bane garuruwan su.
“Za a raba wa karuwan fom din da za su cika kuma gwamnati za ta yi amfani da bayanan da suka bada wajen maida su ga ‘yan uwansu.
“A fom din kowace karuwa za ta fadi irin aiki ko sana’ar da take son yi daga nan gwamnati za ta tallafa da jari.
“Gwamnati za kuma ta yi wa duk karuwan da suke bukatan aure ko ta fito da miji aure a jihar.
“Gwamnati a shirye take domin ganin an kiyaye dokokin shari’a a jihar amma ba tare da an tauye wa wani ko wata hakin ba.
Shugaban kungiyar masu Otel a jihar Patrick Anyawu ya ce akwai gidajen karuwai 41 da ke aiki a wajen garin jihar.
Anyawu ya yi kira ga hukumar Hisbah kada su kori karuwan dake wadanna wurare.
A karshe Hafsat Aliyu wacce ta yi magana a madadin karuwan da aka kirga ta yi kira ga gwamnati da ta cika alkawuran da ta dauka sannan su kuma za su yi kokarin amfani da damar da gwamnati ta basu wajen zama shiryayyun mutane kuma abin moriya wa kansu da al’umma.