An dade ana cewa yara manyan gobe, Daga Muazu Muazu

0

Mutanen nan sun hana mu girma. Sun hana mu dama, sun ki su ba mu wuri mu girma, kamar yadda su aka ba su dama suka girma shekaru da dama da suka gabata. Suna 6ata mana lokaci!

Yanzu da Baba Buhari ya hakura ya yi mulkin nan sau daya, bai dawo a karo na biyu ba (second term). Da sai mu ce sai kuma wane ne ya ke gaban mu ya ke damun mu sai ya hau kujerar mulkin Najeriya? Watakila tsohon mataimakin shugaban kasa ne wato – Atiku Abubakar.

To da shi ma ya zama shugaban kasa a 2019, da yanzu saura shekara biyu mu gama da shi ya sauka mu gwada wani, in ba mu ba shi damar dawo wa a karo na biyu ba kenan.

Wane ne wanin?

Watakila mu ce tsohon gwamnan Kano kuma tsohon sanatan Kano ta tsakiya – Engineer Dr. Rabiu Musa Kwankwaso.

Sai mu ce kai ma zo ka gwada tun da ka ce za ka iya. Shi ma in mu ka ba shi damar ya gwada shekaru hudun sa sai mu ajiye shi. Kenan in haka ta faru a cikin shekaru goma shi biyu mun sallami mutum uku daga Arewa, sai kuma mu koma wani 6angaren na Nigeria mu dauko wani mu gani.

Kowa mulki yake so a kasar nan a ciki har da ni mai rubutu. Rahotanni lokacin za6en 2019 sun rawaito Buhari yana cewa, “Atiku ya bari in gama mana”.

Yanzu kasarmu ta zama ba cancanta a ke kallo ba yayin bada mulki ko zabe, a kowanne irin mukami. Kwata kawai a ke yi, in kana da karfi da daurin gindi a wajen manyan kasa.

Kuma in mutum ya hau ya tashi sauka, sai ya nemo wani wanda shi ma bai cancanta ba ya mika masa mulkin, watakila don yana tunanin ko zai rufa masa asiri kan irin badakalolin da ya tafka lokacin da ya ke kan kujera.

Yanayi yana nuna kamar ba za mu iya farkawa daga nannauyan barcin da muke yi ba.

Allah Ya kawo mana dauki. Ameen.

Muazu Dan Jarida ne dake aiki da Freedom Radio, Kano
08036433199

Share.

game da Author