Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta yi barazanar za ta hukunta duk wata jam’iyyar siyasa wadda ta kasa gudanar da babban taron ta (congress) cikin lumana.
A cikin wata sanarwa da ta bayar a ranar Litinin, INEC ta ce akwai yiwuwar ba za ta amince da sakamakon da aka samar a babban taron jam’iyyar da aka yi a cikin hatsaniya ba idan har ba a daina wannan dabi’ar ba.
Kakakin hukumar, Festus Okoye, ya ce munin rikicin da ake samu a wajen babban taron jam’iyya ya na sanyawa hukumar ta samu “matukar wahala” wajen gudanar da aikin da ya rataya a wuyan ta na kula da jam’iyyun.
Ya kara da cewa ana lalata kayan hukumar a karshe a yayin da kuma rayukan masu shiga taron da na jami’an hukumar ke fuskantar barazana.
Okoye ya ce, “Wannan hukumar ba za ta zura ido ta na kallon yadda ababen takaici da rikice-rikice ke aukuwa a manyan tarurrukan jam’iyyu ba, inda kuma ake barazana ga rayuka tare da barnata kayayyaki.
“Shakka babu, daga yanzu INEC za ta sake duba rawar da ta ke takawa a wadannan abubuwan, idan har su ka ci gaba da jefa rayuwar jama’a da ma’aikatan hukumar cikin had0ari.
“Saboda haka, za a gamu da fushin hukuma sosai a duk lokacin da babban taron jam’iyya ya zama na tada husuma da lalata kayayyakin INEC. Ban da sake mayar da irin wadannan kayayyakin da aka barnata, akwai yiwuwar a soke jam’iyyun daga karbar kayan INEC don gudanar da ayyukan su a nan gaba.
“Haka kuma mai yiwuwa ne hukumar ta janye ma’aikatan ta daga sa ido kan irin wadannan tarurrukan na tada husuma da jam’iyyun ke yi, wanda hakan zai haifar da kin amincewa da jam’iyyar ma kwata-kwata.”
Hukumar ta tunatar da jam’iyyun siyasa cewa akwai zabubbukan share fage da ke tafe inda za su zabi ‘yan takarar su na zabubbukan da za a yi da zabubbukan cike gurbi, musamman zaben gwamnan Jihar Anambra da zabubbukan kananan hukumomin Gundumar Babban Birnin Tarayya (FCT).
Okoye ya ce, “Tilas ne jam’iyyu su tsaya su yi aiki da jadawalin lokutan da aka fitar na abubuwan da za a yi a wadannan zabubbukan kamar yadda hukumar ta fitar da shi, wanda kuma an aika masu shi kuma akwai shi a gidan yanar INEC (www.inec.gov.ng).
“Tilas ne jam’iyyun su tabbatar da cewa zabubbukan su na fidda gwani an yi su cikin lumana da kyakkyawan tsari.
“Abu mafi muhimmanci shi ne tilas su bi Dokar Zabe sau da kafa, da Dokoki da Tsare-tsaren INEC, da kuma kundayen tsarin mulki da ka’idojin jam’iyyun, wadanda hukumar ta na da su a hannun ta.
“A karshe, a wajen gudanar da ayyukan su na cikin gida, tilas ne jam’iyyun siyasa su dauki kan su da daraja kamar yadda su ka kauki hukumar a lokacin zabubbuka, wato su yi komai a bayyane, da tsare gaskiya, da bin dokoki da yin komai cikin lumana.
“INEC na ci gaba da damuwa sosai kan hatsaniya da tada hankali a cikin jam’iyyu ta yadda a yanzu akwai kararraki a kotuna daban-daban waɗanda aka shigar a dalilin manyan tarurruka da zabubbukan share fage da hukumar ta gudanar.
“Duk da haka, hukumar za ta ci gaba da yin aiki da goyon bayan jam’iyyun siyasa wajen tallafa wa ayyukan su na cikin gida domin a gina tsarin dimokiradiyya mai nagarta a Nijeriya.”
Kwanan nan ne dai rikice-rikice su ka barke a wajen manyan tarurruka da wasu jam’iyyu su ka gudanar, musamman ma dai jam’iyyar PDP.
Discussion about this post