‘Yan Arewa masu hada-hadar kasuwanci a Kasuwar Shanu ta Umuchieze a Karamar Hukumar Umunneochi ta Jihar Abia, sun karyata zargin wai su na bai wa ‘yan bindiga mafaka, har ma da masu fashi da makami.
Cikin wata sanarwa da kakakin yada labarai na su mai suna Buba Kedemure ya fitar tare da kiran taron manema labari a ranar Litinin, ya ce zargin da wasu ke yi masu karya ce da sharri da kage marasa tushe.
Ya bayyana cewa ana yayata cewa “wai kungiyar mu ta bai wa wasu batagari iznin kai hare-hare a ciki da wajen jihar.”
Kedemure ya ce to wannan sharri ne kawai, “kuma wasu batagari ne ke kitsa sharrin wadanda ke ciki da wajen kasuwar shanun, domin su haddasa kuma su rura wutar fitina kawai. Kuma su tunzira al’ummar yankin da gwamnatin jihar su yi masu dirar-mikiya.”
Ita dai wannan kasuwar a cewa Buba Kedemure, an kafa ta ne shekaru 16 da su ka gabata, kuma ta zama wuri ko cibiyar da ta hada kawunan ‘yan Arewa da ‘yan kudu.
Ya kara da cewa “wasu mutane ba su farin ciki da irin zaman lafiya da zaman lumanar da ake yi tsakanin al’ummar yankin da kuma ‘yan Arwar da ke gudanar da kasuwanci a kasuwar.”
Kedemure ya kara da cewa kungiyar su ta aika wa Kwamishinan ‘Yan Sanda na Abia da Shugaban SSS wasika tun cikin watan Janairu, ta na sanar da su cewa akwai fa kalubale na matsalar tsaro a cikin kasuwar.
Shugaban Kungiyar ‘Yan Kasuwar Shanu ta Abia, Annayim Umar ya kara da cewa sun a ta kokarin yi wa jama’a nasiha dangane da wajibci da muhimmancin zaman lafiya da juna.
Discussion about this post