Kungiyar kwadago ta ƙasa NLC ta bayyana cewa za ta fara yajin aikin gama gari idan gwaman jihar Kaduna Nasir El-Rufa’i ya ci gaba da shirin sa na zaftare ma’aikatan gwamnatin jihar.
Shugaban kungiyar Ayuba Wabba ya sanar da haka a hira da yayi da PREMIUM TIMES ranar Litini.
Duk da cewa Wabba bai fadi dalilin da zai sa zaftare ma’aikata a jihar Kaduna zai sa a kungiyar za ta kira yajin aikin gama gari a kasa ba, ya ce El-Rufa’i ya karya wasu dokokin korar ma’aikata a kasar nan.
Ya ce kafin a kori ma’aikata irin haka kamata ya yi a sanar da wakilan ma’aikatan wato kungiyar ma’aikata domin tattauna yadda za a biya su kudaden sallama da kuma sanin dalilan da ya sa dole sai an yi wannan kora.
Wabba ya ce a shekaran 2017 gwamnatin jihar Kaduna ta sallami malaman firamare 20,000 a jihar ba tare da ta biyan su kudaden sallaman ma’aikata akalla kashi 90% daga cikin su ba.
Ya kuma karyata yawan kudaden da El-Rufa’i ya ce gwamnati na kashewa wajen biyan albashin ma’aikatan jihar, ya na mai cewa El-rufai ya hada harda kudaden da gwamnati ke biyan ‘yan siyasa da ta nada mukamai.
Wabba ya ce kungiyar za ta zauna ranar Alhamis domin tattauna yadda za a fara yajin aikin gama gari a kasar nan domin ma’aikatan jihar Kaduna.
Ya ce kungiyar ta aika wa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da wasika domin ya ja wa El-Rufa’i kunne game da zaftare ma’aikata da yake shirin yi a jihar Kaduna.
Zuwa lokacin da aka rubuta wannan labari kakakin gwamna El-Rufa’i, Muyiwa Adekeye bai ce komai ba game da wannan batu.
Zaftare ma’aikata a jihar Kaduna
Idan ba a manat ba El-Rufai ya bayyana a hira da yayi da gidajen radiyon jihar cewa, ma’aiakatan jihar da dama basu aikin komai a jihar albashi kawai suke karba.
Kananan hukumomin jihar sun sallami ma’aikata akalla 4000, mako daya kafin a fara azumin watan Ramadana. Bayan haka ya ce gwamnati za ta kori wasu dubban ma’aikatan da basu aikin komai a jihar.