Bankin Bada Lamuni ga Kasashe na Duniya (IMF), ya shawarci kasashen yankin Sahara da su kara kokartawa a cikin kasashen su wajen kara narka wa jama’a harajin samun kudaden shiga daga cikin kasashen na su.
Babbar Daraktan Bankin IMF Kristalina Georgiena ce ta yi wannan shawarar a ranar Laraba a Washington D.C, Babban Birnin Amurka bayan wani taron hadin guiwa tsakanin IMF da Bankin Duniya.
A jawabin da ta yi a taron manema labarai, Georgieva ta tabbar wa yankin kasashen Sahara cewa za su ci gaba da jin dadin lamunin da bankin ke ba kasashen domin inganta ayyukan gwamnati da kuma tabbatar da ana gudanar da ayyuka da gaskiya bisa ka’ida.
“Mun bijiro da tsarin dakatar da kasashe daga biyan basussuka zuwa wani lokaci saboda jigatar da tattalin arzikin su yay i sanadiyyar barkewar cutar koron. Kuma har zuwa yanzu an tsayar da karbar kudaden daga kasashen, wadanda su kai dala bilyan bakwai.
“Sannan kua wasu kasashen Yankin Sahara din an yafe masu basussuka saboda jigatar da tattalin arzikin su ya yi sanadiyyar korona.
“Kuma mu na kokarin ganin an bijiro da tsarin Rage Fatara da Yunwa a yankunan kasashen yankin Sahara.”
Sai dai kuma ta yi gargadin cewa tattalin arzikin duniya a hanlin yanzu ya na cikin Gagarin da manyan kasashe irin su Amurka da Chana ne kadai tattalin arzikin su ked an bunkasa.
Amma inji ta, sauran kasashe musamman marasa karfi tattalin arzikin su sai baya ya ke ci.
Ta ce wannan matsala na kawo barazanar karuwar rashin aikin yi, yunwa, harkallar kudade da karyewar tattalin arzikin wasu masana’antu da kuma shiga garari.
Idan ba a manta ba, a baya PREMUM TIMES HAUSA ta buga labarin cewa Najeriya ta bijire wa shawarar Bankin IMF cewa ta karya darajar naira domin ceto tattalin arziki.
A labarin, Gwamnatin Najeriya ta ki amincewa da shawarar da Bankin Bayar da Lamuni na Duniya (IMF) ya bayar cewa wajibi ne kasar ta karya darajar naira domin ceto tattalin arzikin ta.
Najeriya ta bayyana cewa idan ta yi haka, to jama’a a su kara shiga uku sau uku, domin farashin kayan abinci da kayan masarufi da dukkan kananan kayan amfanin gida ga masu karamin karfi zai hauhawa sosai.
IMF dai ta ce karya darajar naira shi ne zai bunkasa karfin tattalin arzikin masu kananan kasuwanci, domin darajar naira a gaban dala da kudaden kasashen waje irin su fam da Yuro, ba ta kai yadda Najeriya ke tinkaho ta kai ba.
IMF na ganin cewa Najeriya ta tsula wa naira daraja da karin kashi 18 cikin 100, shi ya sa tattalin arzikin kasar ke ci gaba da yin dabur-dabur, dawurwura da kara nausawa cikin kunci da tsadar rayuwar da ake ci gaba a fuskanta a cikin kasar.
“Wannan gurguwar shawara ce, IMF na neman dora kasar nan a kan hanyar da idan aka bi, ba mai bullewa ba ce. Sukuwa IMF ke son dora Najeriya a kan makahon doki.” Inji Najeriya, ta na maimaita cewa karya darajar naira zai kara haifar da tsadar kaya a kasar nan.
Cikin shekarar da ta gabata dai Najeriya ta karya darajar naira domin cike gibin da ke tsakanin arashin kudaden kasashen ketare a kasuwanni, wadanda su ka sha bamban da farashin gwamnati da ake bayarwa a bankuna.
Hakan kuwa ya zo ne sanadiyyar kwankwatsar da annobar cutar korona ya yi wa tattalin arzikin Najeriya, inda aka shafe watanni ’yan kasuwa, masana’antu da cibiyoyin hada-hada da kasuwanni na kulle.
Sannan kuma a lokacin kasuwar danyen mai a duniya ta tsaya cak, ta yadda ko kyauta aka bayar da danyen mai, babu mai bukata. Har ta kai danyen mai bai kai darajar ruwan cikin tulun dan garuwa ba.
Sai dai kuma IMF na ganin har yanzu tsarin sabat-ta-juyat-tar naira da dala a kasar nan da kasashen waje ya hana asusun kasar na waje kara bunkasa, alkadarin sa ba ya da wata muhibba. Haka kuma cikin gida a kullum naira na shan kashi a wajen dala, saboda babu takakaimen farashi, sai irin yadda dala ta ga dama ta ke karkata akalar naira a kasuwa.
A yanzu dai a ma’aunin masu zuba jari da masu hada-hadar kaya daga kasashen waje, naira 398.50 na daidai da dala 1.
Wato kenan a ranar Litinin dala ta tashi daga naira 397.50.
Amma a hannun ’yan canji, su na sayar da dala 1 a kan naira 480.
Shi ya sa IMF ta ce Najeriya ba ta wani takamaimen tsarin da zai iya hana farashin dala dagawa sama, tare da hana naira shan dukan tsiya a hannun dala a kasuwar cikin gida ballantana a kasuwannin kasashen waje.
Gargadin Majalisar Dinkin Duniya Ga Afrika Kan Yawan Ciwo Bashi:
Tulin bashin da kasashen Afrika ke ciwowa ya kamo hanyar jefa nahiyar cikin mummunan yanayi.
Majalisar Dinkin Duniya (UN) ta yi kakkausan gargadin cewa kasashen Afrika na bukatar bijiro da nagartattun tsare-tsare da kuma tallafi daga kasashen duniya, domin kauce wa shiga jangwangwamar mummunar matsalar da yankin ka iya shiga nan gaba kadan, sakamakon tulin bashin da kasashen ke ciwowa ba kai ba gindi.
Cikin wata sanarwa da Sashen Sadarwa Tsakanin Kasashen Duniya na Majalisar Dinkin Duniya ya fitar a ranar Laraba, UN ta yi kakkausan gargadin cewa tattalin arzikin Afrika bai ga komai ba tukunna daga mummunan sakamakon da ka iya biyo bayan annobar korona.
Sanarwar wadda Davi Palanivelu ta sa wa hannu ita da Helen Rosengren ta Sashen Nazarin Tattalin arziki da Walwalar Jama’a, sun bayyana cewa matsalar tattalin arzikin da barkewar cutar korona ya haifar a Afrika zai dade ya na gurzar milyoyin jama’a tare da kassara ayyukan dogaro da kai da kara matsin lambar matsaloli ga marasa karfi.
Kuncin rayuwar da aka shiga lokacin korona zai dade a jikin harkokin tattalin narzikin nahiyar Afrika da kasuwanci da kuma cikin zukatan al’umma.
Sanarwar ta ce tilas sai an mike tsaye domin ganin an bijiro da ingantaccen tsarin da zai kasance tudun dafawa a mike tsaye, yayin da tattalin arzikin nahiyar ya fadi, ya kifa kasa rub-da-ciki.
Karara sanarwar ta nuna matsin tattalin arzikin da ya faru lokacin korona, zai dade tsawon shekaru kafin ya yi bankwana da Afrika. Kuma ko zai yi bankwanan, sai an mike tsaye an bijiro da tsare-tsaren inganta tattalin arziki, ta yadda rayuwar milyoyin jama’a za ta inganta, maimakon harkokin su su karye rugu-rugu.
Wannan matsala dai tuni ta haifar da talauci, fatara, rashin aikin yi, karyewar manya, kanana da matsakaitan sana’o’i, kulle masana’antu, korar ma’aikata, sannan kuma ga gagarimar matsalar kiwon lafiya da ta addabi kasashe daban-daban na Afrika.
UN ta yi cikakken bayanin irin halin kaka-ni-ka-yin da tattalin arzikin manyan kasashen Afrika masu kari uku ke ciki a yanzu. Kasashen su ne Najeriya, Afrika ta Kudu da Masar.
Yunwa Da Tabarbarewar Tattalin Arziki: Gaba Damisa Baya Siyaki:
Baya ga wannan gagarimar matsala sakamakon yawan cin bashi da kasashen Afrika ke yi, a makon da ya gabata kuma Shugaban Bankin Bunkasa Afrika, Akinwumi Adesina da mashahuran masana 24 na duniya sun roki Amurka ta taimaka a kauce wa barkewar yunwa a duniya.
Shugaban Bankin Bunkasa Kasashen Afrika, Akinwumi Adesina da wasu gaggan masana ilmin kimiyya da masana tattalinarziki da mashahuran masu bncike 24 na duniya, sun rubuta wa Shugaban Amurka Joe Biden wasikar neman rokon Amurka ta yi amfani da karfin arzikin ta a kawar da yunwa a duniya, nan da shekarar 2030.
Masanan sun ce ya dace matuka Amurka ta shiga sahun kasashen dunya domin a kawar da yunwa ta hanyar kafa gagarimar cibiya idan an je Taron Majalisar Dinkin Duniya kan Abinci.
“Yayin da duniya ke tafiya da kyar tun bayan dukan tsiya da barkewar cutar korona ta yi, to tun daga wannan shekara ta 2021 ya kamata a fara gagarimin shirin kawar da yunwa a duniya, nan da shekarar 2030.
“Yunwa ta fi yi wa milyoyin mutane barazanar kisa a duniya fiye da cutar korona. Domin idan jikin mutum babu abinci, to magani ma ba zai yi amfani ko tasiri a jikin ba. Abinci da kayan sinadaran gina jiki sun a rigakafin yunwa. Ya kamata mu yi wa duniya rigakafin yunwa.” Inji Adesina.
Farkon wannan makon ne PREMUM TIMES HAUSA ta buga labarin cewa yunwa ta darkako Arewacin Najeriya da wasu kasashe 20.
A ckin labarin, Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (FAO) ta yi gargadin cewa yunwa ta darkako Arewacin Najeriya da wasu kasashe 20 daban-daban na duniya.
Wasu kasashen da hukumar ta FAO ta yi gargadin cewa yunwa ta nausa kuma ta darkaka sun hada da Afghanistan, Yemen, Congo, Sudan, Habasha, Haiti da Syria.
Wadannan kasashe 20 da hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta lissafa, ta ce nan da ’yan watanni za su iya fadawa cikin halin matsananciyar yunwa, idan ba a gaggauta yin wani kokarin cetar da yankunan ba.
Rahoton wanda na hadin-guiwa ne tsakanin FAO da Cibyar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (WFP), ya kuma yi nuni da cewa
nan da watan Yuli wadannan kasashe za su shiga matsanancin karancin abinci, don haka akwai bukatar samar da tallafin gaggawa a wuraren da ake ganin matsalar za ta fi shafa matuka.
Rahoton ya danganta kazamin rikicin da ake yi tsakanin Yemen da Saudiyya ne zai jefa wani yanki na kasar Yemen cikin matsanciyar yunwa da karancin abinci.
“Sama da mutum miliyan 16 a kasar Yemen ka iya fuskantar matsanciyar yunwa da karancin abinci musamman zuwa cikin watan Yuni, 2021.
A Arewacin Najeriya kuwa, rahoton ya ce ana tsoron karancin abinci tsakanin watannin Yuni, Yuli da Agusta, sakamakon rikice-rikicen ’yan bindiga da Boko Haram a Arewacin Najeriya.
Rahoton y ace matsalar da aka fuskanta a shekarar da ta gabata, za ta iya nunkawa a wannan shekara.
“Nan da watanni shida akalla mutm miliyan 13 za su iya afkawa cikin gagarimar matsalar karancin abinci da matsananciyar yunwa a Arewacin Najeriya.” Haka dai rahoton ya tabbatar.
Dama kuma kusan mutum milyan 32 na rayuwar ‘ya-mu-samu-ya-mu-sa-bakin-mu’, kamar yadda rahoton ya jaddada.
A cikin rahoton, Babban Daraktan Abinci na Hukumar FAO, QU Dongyu ya bayyana cewa matsalar da ta tunkari wadannan kasashe abin tayar da hankali ce matuka.
“Ya zama wajinin mu a tashi a gaggauta yanzu-yanzu domin hakan zai iya cetar rayuka dama, kuma za a hana barkewar mummunar matsala.” Gargadin Dongyu kenan.
Yadda Tulin Bashi Ya Hana Najeriya Iya Numfashi Mai Nauyi:
Kwanaki biyu kafin fitar da gargadin da UN ta yi a kan matsalar cin bashin da ta dabaibaye tattalin arzikin kasashen Afrika, PREMIUM TIMES HAUSA ta buga bayanan yadda tulin bashin da Najeriya ke kara yawa a kullum sai kara fitowa su ke yi, inda a yau Litinin kididdigar da Hukumar Kididdigar Alkaluman Bayanai ta Kasa (NBS) ta bayyana cewa ana bin Najeriya bashin dala biliyan 32.92.
NBS ta bayana cewa adadin wadannan kudade duk lissafi ne na iyakar ranar 31 Ga sama, 2020 ba a lisasafa da basukan da su ka kama daga Janairu zuwa Maris da mu ke ciki ba.
NBS ta karayin jawabin cewa
Daga cikin wadannan makudan kudade da ake bin Najeriya bashi, naira tiriiyan 12.71 basussukan kasashe da kamfanoni ko cibiyoyin kasashen waje ne, ne, yayin da naira tiriliyan 20.21 na cikin gida ne.
Wasu manayan cibiyoyin hada-hadar kudade da su fi bin Najeriya bashi, akwai na dala $4.6 na yarjejeniyar da aka kulla da AFD, Exim Bank of China, JICA, India, da KFW. Sai kuma bashin $11.17 Yuro dana dala $186.70 .
Basussukan sun nuna cewa kudaden da ake bin jhohin kasar nan 36 har Abuja, sun kai naira tiriliyan 4.19.
Cikin makonni biyu da su ka gabata, PREMIUM TIME HAUSA ta buga labarin yawan bashin da ake bin Najeriya ya kai naira tiriliyan 32.9
Ofisihin Kula da Basussukan da ake Bin Najeriya ya bayyana cewa lamunin da Najeriya ta kinkimo cikin 2020 ne ya kara wa kudin yawa har ta kai kudin da ake bin Najeriya bashi daidai karshen watan Disamba, 2020, sun kai naira tiriliyan 32.
Ofishin Kula da Basussuka, wato ‘Debt Management Office’ ko DMO a takaice, ya ce tantagaryar kudaden da ake bin Najeriya bashi sun kai naira tirilyan 32.915.
Amma kuma ya ce kudaden da kasar nan ke ciwowa bashi domin aiwatar da ayyukan kasafin kudi a duk shekara, sun ragu ba kamar 2017 da 2019 ba.
Wannan adadin kudade har naira tiriliyan 32.915, sun hada da wadanda Gwamnatin Tarayya ta ciwo, sai kuma wadanda jihohi daban-daban su ka rakito.
Haka kuma a cikin wadannan jimillar kudaden an hada har da wanda Hukumar Babban Birnin Tarayya (FCT) ta kinkimo a matsayin bashi.
Sai dai kuma DMO ta dora dalilin yawan ramto kudaden da aka rika yi a cikin 2020 cewa bullar annobar korona ce ta haddasa hakan.
“Idan za a iya tunawa, bayan Najeriya ta fita daga matsin tattalin arziki cikin 2017, an samu raguwar yawan ramto kudade domin a gudanar da ayyukan kasafin kudi.
“An ramto naira tiriliyan 2.36 cikin 2017, naira tiriliyan 2.01 cikin 2018, naira tiriliyan 1.61 cikin 2019, sai kuma naira tiriliyan 1.59 cikin 2020, duk domin a samu damar aiwatar da ayyukan cikin kasafin kudi na kowace shekara da aka lissafa a sama.
“Ba Najeriya kadai ce ta rika tattago bashi ba saboda kuncin tattalin arziki sanadiyyar barkewar korona. Su kan su manyan kasashen da su ka ci gaba a duniya, sun kara malejin bashin da su ke ciwowa a lokacin.”
DMO ya yi karin hasken cewa akwai bashin cikin gida da ake bin Najeriya wanda ya kai naira tiriliyan 2.3.