KORONA: Hukumar WAEC ba za ta shirya jarabawar karshe na kammala babbar Sakandare ba

0

Hukumar Shirya Jarabawar Kammala babbar Sakandare (WAEC), ta bayyana cewa akwai yiwuwar ba za ta shirya jarabawar na watan Mayu/Yuni a bana ba saboda tangardar da aka samu wajen karatun yara saboda Korona.

Jami’in hukumar Patrick Areghan ya fadi haka ranar Talata a garin Legas da yake sanar da sakamakon jarabawar WAEC din da dalibai masu, zaman kansu ke rubutawa.

Ya kara da cewa hakan ya biyo bayan sauya jadawalin karatun dalibai da nnobar Korona ta kawo a kasar nan.

Areghan ya ce nan ba da dadewa ba hukumar za ta sanar da lokacin da za a rubuta jarabawar.

Ya yi kira ga shugabanni da masu makarantun sakandare da su tabbatar sun yi wa dalibansu rajistar jarabawar domin guje wa fadawa cikin matsaloli a lokacin da za a fara rubuta jarabawar.

Idan ba a manta a shekaran 2020 da cutar korona ta bullo a kasar nan gwamnati ta rufe duk makarantun kasar nan domin kare dalibai daga kamuwa da cutar.

A wancan lokaci gwamnati ta umarci dalibai su ci gaba da karatun su ta hanyar yanar gizo yayin da suke zama a gida.

A dalin annobar Korona, har yanzu ba a samu daidaituwa ba musamma a wuraren hutun di ai, rubuta jarabawa da zangon karatu.

Share.

game da Author