Za a kashe naira bilyan 797.2 domin sake titin Abuja zuwa Kano baki dayan sa – Gwamnatin Tarayya

0

Titin Abuja-Kaduna-Kano da yanzu ake kan aikin gyaran wuraren da su ka lalace, yanzu kuma an ajiye batun gyara za a sake titin baki dayan sa.

A kan haka ne Gwamnatin Tarayya ta amince a kashe zunzurutun kudi naira bilyan 797.2 domin sabunta titin mai nisan sana da kilomita 400.

Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola ne ya bayyana wa manema labarai na Fadar Shugaban Kasa wannan sabon aiki da za a tattago.

Ya ce an amince da sake titin baki dayan sa ne, a wurin taron Majalisar Zartaswa na Ranar Laraba, wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta da kan sa a Fadar Shugaban Kasa.

A wurin taron kuma an amince a sayo motocin kashe gobara da wasu kayyakin da hukumar Kashe Gobara ke bukata.

Fashola ya bayyana cewa aikin gyaran titin Abuja zuwa Kano da a baya za a kashe wa naira bilyan 155 domin a kammala shi, yanzu zai ci naira bilyan 797.2, domin sabon titi garau za a gina gaba daya.

“Na gabatar da wannan bukata kuma an amince za a sake titin Abuja zuwa Kano gaba dayan sa. Ya tashi daga aikin gyare-gyaren wuraren da su ka lalace zuwa sake gina titin baki daya.

“Kenan kwangilar aikin ta tashi daga naira bilyan 155 ta koma naira bilyan 797.2

“Fashola y ace wasu titinan da aka kammala gyarawa kuma nan ba da dadewa ba masu kwangilar za su damka su ga Gwamnatin Tarayya, sun hada da titin Benin-Asaba, Abuja-Lokoja, Kano-Maiduguri, Enugu-Aba, Sagamu-Asaba, Kano-Katsina, Enugu-Fatakwal, Ilorin-Jebba da kuma Lagos-Badagary.

Sai dai kuma Fashola ya ce za a damka wa gwamnati titinan daya bayan daya.

Dangane da titin Abuja zuwa Kano, Fashola ya ce za a fara kammala Kaduna zuwa Zaria mai nisan kilomita 74. Ya ce shi ne za a kammala cikin 2022.

Sai kuma na Zaria zuwa Kano da Kaduna zuwa Abuja ya ce za a kammala shi cikin 2023.

Share.

game da Author