KORONA: WAHO ta tallafa wa Najeriya da maganin rigakafi da na’urorin gwajin Korona

0

Kungiyar WAHO ta yankin Kasashen Afirka ta Yamma, ta tallafa wa Najeriya da kwalaben maganin rigakafi da na’urorin gwajin Korona.

Shugaban kungiyar Stanley Okolo ya ce hakan wani kokari ne agaza wa kasashen yankin Afirka ta Yamma.

Okolo ya ce ECOWAS ta ware dala miliyan 18 domin siyo maganin rigakafin da za ta rabawa kasashen ECOWAS 15.

WAHO ta danka wa mahukunta a Najeriya kwalaben maganin rigakafi, na’urorin gwajin korona da kayan samun kariya na maikatan lafiya ranar Alhamis.

A jawabin sa lokacin karbar wannan kaya, Shugaban kwamitin PTF kuma sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya bayyana cewa wannan shine karo na biyu da kungiyar WAHO ke tallafa wa Najeriya da kaya irin haka.

Shima karamin ministan lafiya Olorunnimbe Mamora ya jinjina yadda aka zabi Abuja a matsayin garin da za a tara kayan tallafin yaki da korona a kasar nan.

Mamora ya yi kira ga mutane da su ci gaba da kiyaye dokokin gujewa kamuwa da cutar domin samun kariya da hana yaduwar cutar.

najeriya ta karba kwalaben maganin Korona miliyan 4 domin mutanenta. Za a fara yi wa malaman asibiti da manyan jami’an gwamnati rigakafin kafinnan a yi wa sauran mutane.

Ana sa ran za a karbi wasu kwalaben maganin miliyan 16 zuwa Mayu, sannan kuma da wani maganin har miliyan 40 zuwa karshen shekara.

Share.

game da Author