APC na kulla tuggun neman kwace Jihar Zamfara

0

Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa kaddamar da haramta gilmawar jiragen sama a Jihar Zamfara ba wata hanyar samar da tsaro ba ce, kawai wani sabon kitsatstsen tuggun kokarin kwace Zamfara ne APC ke yi daga PDP.

Jam’iyyar PDP dai ta zargi APC da shirya makarkashiyar kwace jihar Zamfara da karfin tsiya, ta hanyar fakewa da matsalar tsaro.

PDP ta fitar da sanarwar wannan zargi a ranar Laraba, ta hannun Kakakin Yada Labarai na PDP, Kola Ologbondiyan.

Sabon hargitsi ya barke a Jangebe, a lokacin da jami’an tsaro da jami’an gwamnati ke damka daliban sakandaren Jangebe da aka ceto a hannun iyayen su a ranar Laraba, a harabar makarantar.

A wannan ranar ce kuma Gwamnatin Najeriya ta sanar da haramta shawagi, sauka ko gilmawar jiragen sama a jihar Zamfara.

Matsalar tsaro ta yi kamari a Arewa maso Yamma, inda a cikin watanni biyu aka yi garkuwa da dalibai sama da 600 a jihohin Katsina, Zamfara da Neja.

Sai dai kuma PDP ta ce Gwamnatin Buhari ta kafa dokar ce ba don saboda matsalar tsaro ba, sai don wata biyan bukata ta siyasa kawai.

“Jam’iyyar mu ba ta yarda da duk wani yunkuri ko tuggu da makarkashiyar da wasu wadanda su ka yi mankas da giyar mulki za su yi a Zamfara ba, ta hanyar dakile dimkoradiyya domin takure gwamnatin jiha.

“Ba mu yarda a nuna ko a dora laifin matsalar tsaron Zamfara a kan Gwamna Bello Muhammad Matawalle, alhali gwamnatin tarayya ta APC c eke da laifin kasa samar wa jihar tsaro da zaman lafiya.

“Dama kuma mu na sane da cewa an dade ana kokarin harmutsa mulkin Gwamna Bello Matawalle, tun bayan da Kotun Koli ta damka masa nasarar zanem gwamnan jihar Zamfara. Abin ya kara tafarfasa bayan da su ka nemi Matawalle ya koma APC, shi kuma yacce ba zai koma ba.”

“Abin da ke faruwa a Zamfara, alama ce da ke nuna cewa Gwamnatin Buhari da APC sun ji kunyar duniya, domin sun kasa samar wa jama’a tsaron da su ka rika cewa za su samar.

”Abin damuwa ne a ce Fadar Shugaban Kasa za ta kauda kai ga abin da ke faruwa a jihohin Neja, Kaduna da Katsina, jihar haihuwar Shugaban Kasa, inda kisan jama’a da garkuwa ya ke kara kamari a kowace rana, sannan ta maida hankali kan Jihar Zamfara wai can ne za a kakaba doka.

Jam’iyyar ya ce irin wannan son rai da rashin adalci da gwamnatin APC ke yi har a batun tsaro, ba shi ne zai iya kai gwamnatin ga samar da mafitar tabbatar da tsaro a kasar nan ba.

Share.

game da Author