MATSALAR TSARO: Mu Tashi, Tashi Mu Farka, Mu Tsaya Mu Dage, Mu Kare Kan Mu, Daga Adamu Kaloma

0

Alummar mu na cikin halin firgici da rashin natsuwa da fargaba domin cigaba da hauhawan matsalar TSARO a kauyuka da biranen Arewacin kasar nan.

Matsalar Tsaro Yana haifar da tabarbarewar duk Alummar da matsalar ya shafa da makwabtan su. Abun Takaici matsalar Sai cigaba da fadada yakeyi Yana iske ko wani lungu da sako.

Abun Takaici, matsalar ta na cin Alummar mu ne da Tallafin Alummar mu. Muna ganin Farkon matsalar mu kasa tashi mu Kare kanmu, Muna Zargin cin amana daga Cikin mu Muna shiru. Muna rufe sharri a cikin mu ba tare da neman magance ta ba.

Tabbas hakan bazai Zama abun da zai haifar Mana da da Mai Ido ba. Ya Zama wajibi ga Iyayen mu, Matasan mu, Shuwagabannin mu da kowa da kowa mu bude idanun mu mu FARKA mu dauki matakan Kare kanmu.

GYARA KAYANKA

Malam Bahaushe yace bazai Zama sauke mu raba ba.

Tabbas ko wace Alumma, Kauye da Birni a FARKA a bacci, a Nemi mafita ga matsalar Tsaro.

Ko wace Alumma su Gina Aikin saka Kai tsakanin Matasan su na duba da Kare Alummarsu a kowani lokaci.

Gina Katangar fahimta da hukuman Tsaro domin Sanar da sahihan labarai domin daukan mataki na gaggawa.

MU FARGA

Kafin wankin hula ya Kai mu dare, ya Zama wajibi mu tashi mu tsaya mu Kare kanmu da kanmu. Mu tashi mu Kare kanmu.

Rufe sharri guda Daya Kan haifar da Matsalar da ba’a San iyakar ta ba. Kamar bakar ashana ne, guda Daya Kan Kona Gari. Idan kana tunanin rufe sharrin Mai sharri shi ne mafita Tabbas kasan gobe sharrin Kai zai ci ba kowa ba.

Sarakuna da Malamai Sai sun zage damtse domin tsayuwa ganin sun kafa tubalin Gina ko wace Alumma.

Share.

game da Author