Sojojin Najeriya na ci gaba da ragargazar ‘yan bindiga a dazukan Kaduna, sun kashe mutum 4 a Chikun

0

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna Samuel Aruwan, ya bayyana cewa dakarun Najeriya sun kashe wasu mahara a karamar hukumar Chikun, sun kuma raunana wasu da dama duk a wannan hari.

Sojojin sun yi wa mahara luguden wuta daga sama a lokacin da suka hango su suna kokarin arcewa bayan sun ji rugugin harsashin jiragen yakin sojojin saman Najeriya a wannan dazuka.

An kashe mutum hudu daga cikin su sannan wasu da dama sun samu raunuka a jikin su.

Bayan haka kuma sanarwar ta kara da cewa mayakan saman Najeriya sun yi aman wuta a wasu sansanonin ‘yan bindiga dake dazukan Karamar Hukumar Birnin Gwari.

A nan yan bindigan ba su sha da dadi ba domin da yawa cikin wadanda suka fatattaka sun arce dauke da munanan rauni a jikin su.

Share.

game da Author