Safiyar Lahadin nan Sojojin Najeriya sun tsayar da motocin da ke tafiya Maiduguri zuwa Damaturu kusan sa’o’i uku, daidai lokacin da su ke barin-wuta da wasu ‘yan Boko Haram din da su ka kai wa sansanin sojoji hari a kusa da Jankana, kauyen da ke kusa da Maiduguri.
Bayan sun gama bata-kashi ne kuma sojojin su ka yi wa jerin gwanon motocin matafiya rakiya zuwa Damaturu.
Wata majiyar cikin sojoji ta bayyana cewa an yi artabu a Boko Haram in a kauyen Lawan-Maigari, kilomita biyu kusa da Jakana.
An ce sun kai hari ne a wani sansanin sojoji, amma an fatattake su.
Jakana gari ne da ke da tazarar kilomita 41 zuwa Maiduguri daga Damaturu, kuma a cikin shekaru 10 da su ka gabata, Boko Haram sun sha kai masa farmaki.
Wani dan bangar bijilante da ke garin Jakana ya shaida wa wakilin mu cewa sojoji sun tsaida zirga-zirgar motoci ne sama da sa’o’i uku domin kada yakin ya ci rayukan fararen hula.
“Boko Haram sun fito ta hanyar Lawan-Mainari, domin su kai wa sansanin sojoji hari. Sai dai kuma sojojin sun yi fito-na-fito da su tsawon awa daya.
“Ba mu tabbatar ko sun gama fatattakar Boko Haram din ba, domin har lokacin da mu ke maganar nan da kai ba a bude hanyar ba.”
Akwai ma wani babban jami’in soja da ya tabbatar wa PREMIUM TIMES wannan artabun, amma ya ce kada a ambaci sunan sa. Sai dai bai yi wani karin haske a kai ba.
“Abin da kawai na tabbatar shi ne sojojin mu na can na aramgama da Boko Haram masu neman tayar da rudani a kan babban titi.” Inji shi.
Shi ma Kwamandan Jami’an RRS na Ko-ta-kwana a Jihar Barno, Abioye Babalola, ya tabbatar da artabun.
Ya ce an fatattaki Boko Haram din, kuma tuni sojoji sun yi wa jerin gwanon motocin matafiya rakiya har zuwa Damaturu, Babban Birnin Jihar Yobe.
“Farmaki ne Boko Haram su ka kai wa sansanin sojoji da ke tsakanin Jakana da Mainok.” Inji shi.