Daya daga cikin Manyan Alkalan Kotun Kolin Najeriya, Sylvester Ngwuta ya mutu safiyar Lahadi ya na cikin barci.
Ngwuta ya rasu ranar 7 Ga Maris, kwanaki 21 kafin ranar da ya shirya zai yi ritaya daga aikin alkalanci. A ranar ce zai cika shekaru 70 a duniya.
Ranar 30 Ga Maris mai zuwa ce Ngwuta zai cika wa’adin ranar yin ritayar sa daga aikin gwamnati, kuma tuninya shirya yin ritaya a ranar.
Wata sanarwa da Rajistara ta Kotun Koli, Hadizatu Mustapha ta fitar a ranar Lahadi, ta bayyana cewa Ngwuta ya mutu wajen karfe 2:30 na dare, ya na cikin barcin da bai sake farkawa ba.
Ta kara da cewa kafin rasuwar sa an kwantar da shi Babban Aibitin Kasa na Abuja, tsawon mako daya.
Hadiza ta kara da cewa yayin da ciwon sa ya yi tsanani, sai aka maida shi bangaren masu jin-jiki sosai, amma kuma an tabbatar da yi masa gwaji, ba shi dauke da cutar korona.
“Yanzu dai an killace gawar sa a dakin ajiye gawarwakin asibitin, har zuwa lokacin da za a rufe shi a kabari.”
Ngwuta dai dan asalin jihar Ebonyi ne. Ya zama Mai Shari’a a Kotun Koli cikin watan Maris, 2011. Shi ne ya zartas da hukuncin shari’ar tankiyar zaben 2019 na gwamnan jihar Kano, tsakanin dan takarar PDP Abba Gida-gida da kuma Gwamna Abdullahi Ganduje na APC.
Ya na daya daga cikin manyan alkalai wadanda EFCC ta kai farmaki gidajen su cikin 2017, bisa zargin su da harkallar makudan kudade.