Modupe Oyetosho da ta fara noma kamar da wasa domin kara samun abin taimakawa ga kudaden da ta ke dan samu, a cikin shekara bakwai sai ga wannan mata mai himmar noma eka 5 ta kai ga ta na noma eka 5000 a duk shekara.
Ta bayyana cewa ilmin fasahar da ta samu ne ya kai ta ga wannan gagarimin nasibin noma, ta hanyar amfani da kayan noma na zamani a Jihar Edo da Jihar Oyo.
Da eka biyu ta fara, wadda ta karba jingina daga hannun mahaifin ta. Daga nan sai ta kai ga eka 500, inda yanzu kuma ta kai ta na noma gonaki masu fadin eka 5000.
Zaman yanzu ta na da ma’aikata 25 na dindindin, da kuma wasu mutum 100 masu yi mata aikin wucin-gadi.
Sai dai kuma shekaru uku na farko da Modupe ta shiga harkar noma, ba ta samu ribar ko sisi ba, har sai da wata kawar ta shigar da ita wani tsarin zuba jarin bunkasa sana’a tukunna.
Modupe ta samu nasibin rika kai wa kamfanin yin Indomie rogo da kuma wasu kayan kiwon kaji tukunna.
Sannan kuma ta rika noma waken soya domin wasu masana’antun yin filawa.
Ita ce Shugabar Anchor Farm, amma an fi sanin sa da Smart Farm.
Gonar Mopude ta yi fadi da yawan da ta kai sai dai ta rika yin amfani da na’urar ‘drones’ domin’ duba lafiya da halin da amfanin gonar ke ciki.
Ta bayyana cewa a jirin na’urar ‘drones’ din ta akwai na’urar da ke tantance lafiya ko akasin haka g auk wata shukar da ke gonakin ta.
Sai dai kuma ta nuna takaicin yadda ta rasa saurayin da za su kulla aure a cikin gonar ta da ta ce a ciki ya rasu, cikin shakarar 2020.
“Abin da ya fi bakanta min rai shi ne, wannan saurayi nawa, a cikin gona ta masu garkuwa da mutane su ka kama shi. Ina kan hanyar zuwa gonar su ka kashe shi.
“Abin farin ciki kuma dangane da wannan harkar noma, shi ne yadda na samu nasibin da har manyan kungiyoyi na kasashen sun a cikin kwastomomin da ke sayen mfanin gona daga hannun ta.
“Ka ga a yanzu haka ni na ke sayar wa kamfanin Indomie filawar alkamar da su ke amfani da ita.
“To kuma ina ganin akwai bukatar Najeriya ta canja takun shirin samar da abinci. Saboda nan zuwa shekarar 2030 yawan ‘yan Najeriya zai iya kai mutum bilyan 450. Saboda a yanzu mun kai mutum milyan 200, kuma akasari mun dogara ne ga abincin da mu ke ci duk shigo da shi ake yi daga waje. Shin ya ka ke ganin idan mu ka ka kai shekarar 2030 kuma?
“Saboda haka gaskiyar magana akwai bukatar mutane masu yawa su kara shigowa harkar noma, domin a kara samun hanyoyin kara yawan abinci a kasar nan. Ga shi dai kusan kashi 70 na ‘yan Najeriya a yanzu haka manoma ne, amma kuma ba mu iya fitar da kayan abinci wasu kasashen duniya.
Ta kuma nuna muhimmancin amfani da kayan noma na zamani idan ana bukatar bunkasa harkokin noma har a samu wadata da yalwar abinci a kasar nan.
Discussion about this post