Shugaban marasa rinjaye a majalisar Dattawa, Sanata Abaribe, kuma jigo a jam’iyyar PDP sannan kuma dan asalin jihar Abia ya yi tir da komawar tsohon babban hafsan sojojin Najeriya, Janar Ihejirika jam’iyyar APC.
Janar Ihejirika mai ritaya ya canja sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC, hakan wanda kakakin shugaban riko na jam’iyyar Mohammed Mamman ya sanar a wata takarda da shugaban riko na jam’iyyar, Mala Buni ya saka wa hannu ranar Juma’a.
Takardar ya ce tuni har an mika Ihejirika ga kwamitin jam’iyyar dake wanke sabbin shigan jam’iyyar karkashin jagorancin gwamnan jihar Jigawa Abubakar Badaru da Farouk Adamu Aliyu.
” Ace wai su Ihejirika ne ke shiga jam’iyyar APC bayan maida su ‘ya’ya da PDP ta yi. Ta wanke su tas-Tas ta mulke su da gangariyar mai, suka ci moriyar ganga, yanzu kuma, an watsar da PDP, Ihejirika ya koma APC.
” Wannan rashi kunya har ina? Zan ga yadda za a ce wai yau Ihejirika ne a jihar Abia zai fito ya rika tallata APC a gaban mutanen jihar Abia.
” Jam’iyyar APC ta maida mu bayi, mu yan yankin Kudu Maso Gabas, wato Inyamirai, jam’iyyar APC ta guntule mana fukafukai, ba a damawa da Inyamirai a wannan gwamnati amma kuma yau su Ihejirika ne ke shiga irin wannan jam’Iyya.
Wadannan sauye-Sauye da ake ta samu a musamman wasu daga cikin manyan yan kabilar Igbo na da nasaba da hango kujerar shugabancin Najeriya a 2023, a lokacin da ake kyautata zaton APC za ta mika wa wani dan kudu ne kujerar shugabancin kasar.