FAO na bukatar dala bilyan 1.1 domin magance matsalar abinci a duniya

0

Hukumar Abinci ta Duniya, da ke karkashin Majalisar Dinkin Duniya, ta bayyana cewa ta na bukatar dala bilyan 1.1 da gaggawa, domin dakile yunwa da karancin abincin da ya tunkaro duniya gadan-gadan.

FAO ta kuma bayyana cewa akalla akwai mutum milyan 135 a duniya masu fama da matsanancin karancin abinci.

Ta ce wadannan dimbin milyoyin jama’a na fama da rashin cin yau ballantana na gobe, wanda hakan barazana ce sosai ga rayuwar su da kuma duniya baki daya.

An dai buga wannan rahoto a ranar Alhamis, wanda ke nuni da sama da mutum milyan 48.9 na rayuwa ne a bisa tallafin aikin noman da ake bayarwa domin bunkasa hanyoyin samar da abinci da kuma kayan gina jiki.

Rahoton ya ce yayin da duniya ke ci gaba da juriya da zaman fama da kuncin rayuwa sama da shekara daya, a halin yanzu akwai bukatar samar da dala bilyan 1.1 domin kawar da barazanar rashin abinci a duniya, wadda ke fuskantar sama da mutum milyan 135.

“Ba wani abu ya kara ta’azzarar wannan bala’in yunwa da karancin abinci ba, sai barkewar annobar korona a fadin duniya. Sannan akwai kashe-kashen da su ka haifar da tsaikon noma saboda karancin tsaro a wasu kasashe da kuma ambaliyar ruwa da annobar farin-dangon da aka yi a wasu kasashe tun kafin a girbe amfanin gona. Wadannan sabubba ne da su ka kara haifar da yunwa a kasashen masu karamin karfi a duniya.” Haka rahoton ya bayyana.

Dominique Burgeon, wanda shi ne Daraktan Samar da Abincin Gaggawa na FAO, ya ce “wannan kuncin da aka shiga cikin 2020, shi ne zai ci gaba da adddamar milyoyin jama’a a fadin duniya har bayan shekarar 2021, idan ba matakin gaggawa aka dauka ba.”

Daga nan ya kara da cewa mafi tausayi daga ba’arin jama’a su ne kananan yara da maza da mata kanana masu dan tasawa wadanda kashe-kashe da rigingimun dasu ka ki ci su ka ki cinyewa ke ci gaba da shafar su a kasashe da dama a duniya.

Milyoyin manya da kananan yara dai a kasashe daban-daban na ci gaba da zaman gudun hijira cikin tsakanin rayuwar kunci a fadin duniya.

Share.

game da Author