Malamai uku aka yi garkuwa da, babu dalibi ko daya da mahara suka arce da – In ji Aruwan

0

Kwamishinan Tsaro Da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna Samuel Aruwan ya tabbatar da garkuwa da aka yi da wasu malaman makarantar firamare dake Rama, Birnin Gwari.

Aruwan wanda ya gana da manema labarai a Kaduna ranar Litini, ya ce maharan sun iske malamai ne da wasu tsirarun dalibai a lokacin da suka dira makarantar.

Malamai uku suka tafi da su,babu dalibi ko daya da suka sace.

Malaman da aka sace sune Rabiu Salisu, Umar Hassan, da Bala Adamu.

Dalibai biyu ne suka arce cikin daji a lokacin da suka hangi maharan sun tunkaro makarantar, daliban kuwa sune, Ahmed Halilu da Kabiru Yahaya.

Babu dalibi ko daya da maharan suka yi garkuwa da a wannan farmaki da suka kai makarantar firamaren.

” Ina mai farincikin shaida muku cewa an gano dalibai biyu da suka arce wato Ahmed Halilu da Kabifu Yahaya a lokacin da mahara suka zo makarantar. Baya ga malamai ukun da aka tafi da su duka daliban makarantan na nan cif-cif.

Bayan Ayan haka an gano cewa maharan sun sace shanu masu yawa da baburan hawa da kuma wasu abubuwa masu amfani a wannan hari.

Bayan haka kuma Aruna ya ce, jami’an tsaro sun cinci wani yaro a cikin daji ya a watangaririya bai san inda za shi ba. Wannan yaro mai suna Adewale Rasaq ya arce daga hannun yan bindigan da suka yi garkuwa da shi ne a lokacin da iyayen sa ke tattauna biyan naira miliyan 15 da yan bindiga suka nema a dajin dake karamar hukumar Chikun.

Haka kuma jami’an tsaro sun tsinci wata yarinya mai suna Fatima Lawal a dajin Kauru tana watangaririya. Ita ma ta arce daga hannun wadanda suka yi garkuwa da ita ne kafin abiya kudin fansa.

Aruwan ya ce za a mika yaran ga iyayen su.

Share.

game da Author