Tsohon mataimkin shugaban kasa Atiku Abubakar, ya gargadi masu mulki a Najeriya da ayi taka tsantsan wajen biyan kudin fansa ga ‘Yan bindiga.
Atiku ya ce idan ba a maida hankali an kuma yi taka tsantsan wajen biyan Kudin fansa ga’ Yan bindiga ba za a fada cikin wani hali da fita daga ciki zai yi wuya a kasar nan.
” A ganina kuma shawara ta ga gwamnatocin Najeriya shine a saja dokar ta bace a bangaren ilimin kasar nan. A saka jami’an tsaro a makarantu kasar musamman a yankunan da yan bindiga su ka addaba.
” Dama kuma Najeriya ce ta fi yawan yaran kananan da basu makaranta a duniya. Wannan rashin taro ga dalibai, ya sa za a dad fadwa cikin halin kakanikayi musamma a bangaren ilmantar da yaran a kasar nan.
Idan ba a manta ba, a safiyar Litini, mahara suka yi wa makaranta Firamare dak eRema, Karamar hukumar Birnin Gwari, diran mikiya, suka arce da dalibai da wasu malaman makarantar da haryanu ba a san yawan wadanda suka tafi da su ba.
Wannan abin bakin ciki ya auku ne adaidai ana jimamin wasu daliban da ke tsare hannun yan binda haryanzu ba a ceto su ba.
Maharan sun bukaci a biya su naira miliyan 500 kudin fansa.