Boko Haram sun sako Faston cocin EYN da suka yi barazanar kashe shi da suka yi

0

Boko Haram sun sako faston cocin EYN Bulus Yikura da suka yi garkuwa dashi a makon jiya.

Jami’an tsaro sun bayyana wa wakilin PREMIUM TIMES cewa an sako Yikura da misalin karfe 6:15 na safe inda aka ajiye shi a kusa da garin Maiduguri.

Idan ba a manta ba a makon da ya gabata Boko Haram sun fitar da wani bidiyo inda a bidiyon Yikura ya yi kira ga gwamnati, kungiyar CAN da cocin EYN da su taimaka su ceci rayuwarsa.

Yikura ya ce Boko Haram sun bashi wa’adin kwanaki bakwai daga ranar 24 ga Fabrairu zuwa hudu ga Maris ko su kashe shi.
Wa’adin kwanaki bakwai din ya kamata ya kare a yau Laraba.

Rundunar tsaro ta shaida cewa cocin EYN da iyalen Yikura ne suka shiga suka fita wajen Boko Haram sun sake Faston.

Da yake tattaunawa da PREMIUM TIMES Yikura ya mika godiyarsa ga Allah yadda ya kubutar da shi daga hannun Boko Haram lafiya.

Share.

game da Author