Mahukunta a kasar Saudiyya sun bayyana cewa bana duk wanda zai zo aikin hajji kasar Saudiyya, sai an yi masa rigakafin Korona kafin gwamnati ta barshi ya shiga kasar.
Ministan kiwon lafiyar kasar Tawfiq al-Rabiah ya sanar da haka ranar Litini.
Tawfiq al-Rabiah ya ce daga yanzu yin allurar rigakafin korona na daga cikin sharuddan da baki za su rika cikawa kafin su shiga kasar yin aikin hajji ko Ummrah.
A sanadiyyar yaduwar annobar Korona da duniya ta yi fama da shi, a shekarar 2020, kasar Saudiyya ba ta amince wasu daga wajen kasar su ziyarci kasar yin aikin hajji ko umrah ba.
Baya ga saka dokoki da gwamnatin kasar ta sa da tabbatar da an bi ka’idojin korona, duk da haka ko a kasar mutane kadan ne aka bari su ziyarci wasu muhimman wurare a kasar da suka hada da masallcin Makka da na Madina.
A Najeriya kason farko na kwalabem maganin allurar rigakafin korona sun iso a wannan mako. hukumar Kiwon Lafiya ta aiko da kwalaben rigakafin Korona har miliyan 4 domin a fara yi wa yan Najeriya, kafin waso kwalaben maganin rigakafin su iso a watan mayu.
Gwamnati tace tana sa ran za a yi wa mutane akalla miliyan 70 zuwa shekarar 2022 rigakafin a Najeriya.