Wasu ’yan bindigar da aka hakkake cewa Boko Haram ne, sun yi wa wani sansanin sojoji dirar mikiya a ranar Talata, kuma su ka banka masa wuta, a Katarko, wani kauye da ce cikin Karamar Hukumar Gujba, a cikin Jihar Yobe.
Kauyen Katarko dai ba shi da tazara sosai daga Damaturu, babban birnin Jihar Yobe.
Nisan kauyen bai wuce tazarar kilomita 25 tsakanin sa da Damaturu ba.
Baya ga sansanin sojojin da su ka banka wa wuta, Boko Haram sun kuma banka wa wata makarantar firamare wuta.
Makarantar da su ka banka wa wutar dai dama sun taba kone ta kurmus, tun cikin 2013.
Sai shekarun bayan-bayan nan ne aka gyara makarantar da kudaden Tallafin Wadanda Boko Haram su ka Jikkata.
Wasu rahotannin da ba a kammala tabbatarwa ko tantancewa ba, sun nuna cewa wata kungiyar agaji ce ta ajiye abincin da za ta raba wa wadanda Boko Haram su ka talauta.
To sai dai kuma Boko Haram sun samu lamabin an adana abinci a cikin ajujuwan makarantar domin rabawa.
Wannan ne dalilin da ya sa su ka kai wa makarantar hari, sannan kuma su ka kwashe tulin kayan abincin da aka adana domin raba wa mabukata.
Mazauna kauyen Katarko sun kuma bayyana cewa Boko Haram sun kai farmaki a wani ofishin kula da marasa lafiya, a kauyen na Katarko har su ka kwashe magungunan da ke ciki karkaf din su.
Wani mazauni kauyen mai suna Modu Katarko, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa Boko Haram sun dira kauyen wajen karfe 5:30 na asubahi ranar Talata, su ka rika barna har tsawon sama da awa daya, babu wani jami’in tsaron da ya tunkare su.
“Mu dai kawai sai mu ka rika jin ana kwala kabbara, ana Allahu Akbar! Allahu Akbar! Daga nan kuma sai su ka rika yin ruwan harbe-harbe kawai ko ra ina. Lamarin ya faru jim kadan bayan kammala sallar assubahi.
“Sun kuma kone sansanin sojoji, makaranta da ifishin kula da lafiya kurmus.” Inji Modu.
Harvyanzu dai ‘yan sanda ko sojoji babu wanda ya fitar da sananrwar abinda ke faruwa.
Kakakin zaratan ‘Operation Lafiya Dole Sashe na 2, Kenndy Anyawu bai amsa kira ko sakon kar-ta-kwana da wakilin mu ya aika masa ba.