Hukumar EFCC ta umarci masu bankuna da ma’aikatan bankin da gaggan masu hada-hadar cibiyoyin hada-hadar kudade cewa kowa ya bayyana yawan kadarorin sa, daga ranar 1 Yuni, 2021.
Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa ne ya bayar da wannan umarni, a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a Fadar Shugaban Kasa.
Ya yi wannan umarci a matsayin sanarwa ga manema labarai, jin kadan bayan da ya kammala ganawar sirri da Shugaba Muhammdu Buhari.
Bawa ya bayyana cewa akwai damuwa sosai ganin yadda wasu gaggan masu laifi ke hada kai da bankuna da ma’aikatan bankuna su na karkatar da kudaden su.
“EFCC na bai wa ma’aikatan bankuna umarnin cewa daga ranar 1 Ga Yuni, 2021 hukumar za ta rika tambayar su takardar shaidar bayyana kadarorin su. Kuma dukkan masu bankuna da ma’aikatan su su tabbatar da sun bi wannan umarni.” Inji Bawa.
Cikin wata sanarwa da Kakakin Yada Labarai na EFCC, Wilson Uwujaren, ya ruwaito Bawa na cewa wannan umarni an yi shi ne bisa ka’idar da Dokar Bayyana Kadarori ta 1986 ta gindaya, da nufin tsaftace harkokin hada-hadar kudade a kasar nan.
Ya ce za a rika daukar tsauraran matakan toshewa da dode duk wata kafar da ake bari wasarere, har masu harkalla na samu sun a karkatar da makudan kudade.
Dokar Wajibcin Bayyana Kadarorin Ma’aikatan Bankuna Sashe na 1 da na 7 ta 1986, ta tilasta wa masu aiki bankuna su rika bayyana kadarorin su da zarar sun fara aikin banki. Kuma duk shekara su rika sabunta bayyana kadarorin na su.
“Laifi ne babba ga duk wani ma’aikacin banki ya mallaki kadarorin da su ka zarce adadin albashin da ake biyan sa.” Inji Bawa.
Ya kara da cewa hukuncin wanda ya karya wannan doka shi ne daurin shekaru 10, kamar yadda Sashe na 7(2) na dokar ya tanadar.
“Idan aka kama ma’aikacin banki ya yi karyar adadin kadarorin da ya mallaka, to za a daure shi shekaru 10 a kurkuku, kuma Gwamnatin Tarayya za ta kwace kadarorin.”
Bawa ya nuna damuwa ganin a wani bangaren aikata laifuka kuma, yadda matasa ke kara fantsama cikin aikata zambar kudade ta intanet, wato ‘cybercrime’.
Sai ya shawarci iyayen matasan kasar nan su rika sa-ido da kula da kuma kara tsautsara tarbiyya ga yaran su.