Ofisihin Kula da Basussukan da ake Bin Najeriya ya bayyana cewa lamunin da Najeriya ta kinkimo cikin 2020 ne ya kara wa kudin yawa har ta kai kudin da ake bin Najeriya bashi daidai karshen watan Disamba, 2020, sun kai naira tiriliyan 32.
Ofishin Kula da Basussuka, wato ‘Debt Management Office’ ko DMO a takaice, ya ce tantagaryar kudaden da ake bin Najeriya bashi sun kai naira tirilyan 32.915.
Amma kuma ya ce kudaden da kasar nan ke ciwowa bashi domin aiwatar da ayyukan kasafin kudi a duk shekara, sun ragu ba kamar 2017 da 2019 ba.
Wannan adadin kudade har naira tiriliyan 32.915, sun hada da wadanda Gwamnatin Tarayya ta ciwo, sai kuma wadanda jihohi daban-daban su ka rakito.
Haka kuma a cikin wadannan jimillar kudaden an hada har da wanda Hukumar Babban Birnin Tarayya (FCT) ta kinkimo a matsayin bashi.
Sai dai kuma DMO ta dora dalilin yawan ramto kudaden da aka rika yi a cikin 2020 cewa bullar annobar korona ce ta haddasa hakan.
“Idan za a iya tunawa, bayan Najeriya ta fita daga matsin tattalin arziki cikin 2017, an samu raguwar yawan ramto kudade domin a gudanar da ayyukan kasafin kudi.
“An ramto naira tiriliyan 2.36 cikin 2017, naira tiriliyan 2.01 cikin 2018, naira tiriliyan 1.61 cikin 2019, sai kuma naira tiriliyan 1.59 cikin 2020, duk domin a samu damar aiwatar da ayyukan cikin kasafin kudi na kowace shekara da aka lissafa a sama.
“Ba Najeriya kadai ce ta rika tattago bashi ba saboda kuncin tattalin arziki sanadiyyar barkewar korona. Su kan su manyan kasashen da su ka ci gaba a duniya, sun kara malejin bashin da su ke ciwowa a lokacin.”
DMO ya yi karin hasken cewa akwai bashin cikin gida da ake bin Najeriya wanda ya kai naira tiriliyan 2.3.