Shugaban hukumar ma’aikatan jihar Kano Engr. Bello Kiru ya bayyana cewa gwamnati ta amince da karin girma wa wasu ma’aikatan jihar har 130.
Kiru ya shaida wa Kamfanin dillancin labaran Najeriya a Kano, inda ya bayyana cewa hakan zai kara wa ma’aikatan kwarin guiwar yin aiki a koda yaushe.
Bayan haka, Kiru ya kara da cewa gwamnatin jihar za at ci gaba da yin haka akai-akai domin kara wa ma’aikatan jihar karfin guiwa a aikin su a jihar.