2023: Zan so na zama shugaban Najeriya – Fayose

0

Tsohon Gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose, ya sake jaddada muradin san a ganin an wayi gari ya zama shugaban kasa a 2023, idan har ya samu dama.

Fayose ya ce babu ruwan sa da batun tsayawa takarar Bola Tinubu a karkashin jam’iyyar APC.

Da aka tambaye shi batun zaben 2023, sai Fayose ya ce shi dai ya san cewa jam’iyyar da ya ke ciki, wato PDP za ta iya samar da shugaban kasa a zaben 2023, idan wa’adin Shugaba Muhammadu Buhari ya kare.

“Bola Tinubu dai jagora ne a yankin Kudu Maso Yamma. Amma ni dai nan da shekaru uku da su ka gabata ban gan shi sa ido da ido ba. Sannan kuma tun da na ke ban taba yin magana da shi ta waya ba.

“Saboda haka ban san dalilin da ya sa wasu ke ta kokarin kulla wani kusancin siyasa tsakani na da shi Tinubu ba.

“Ni dai ba dan APC ba ne, kuma ba ni da karfin nada masu wanda za su tsayar takara. Ni muradi na a ce PDP ce ta yi nasara a zaben 2023 kawai.

A wannan hira da ya yi da manema labarai, Fayose ya sake jaddada cewa zai so a ce ya zama shugaban Najeriya.

“Ofishin Shugaban Kasa ofis ne mai daraja da martaba. Zan so a ce ga ni a ciki, na zama shugaban Najeriya.”

Cikin 2017 Fayose ya taba furta bukatar sa ta zama shugaban Najeriya, idan ya samu dama.

Sannan kuma cikin 2020, a lokacin bikin taya shi murnar cika shekaru 60 a duniya, Fayose ya ce zai so zama shugaban kasa, ko kuma wani gawurtaccen mai wa’azi.

Share.

game da Author