Abinda Buhari ya tattauna da sabon shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa

0

A ranar Alhamis, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi ganawar farko da shugaban hukumar EFCC Abdulrasheed Bawa.

Idan ba a manta ba a ranar Laraba ne majalisar Dattawa ta amince da nadin Abdulrasheed Bawa a matsayin sabon shugaban hukumar EFCC.

Bawa ya maye gurbin Ibrahim Magu.

Bawa ya bayyana fadar shugaban kasa domin ganawa da shugaba Muhammadu Buhari a karon farko kafin ya fantsama farautar barayin gwamnati.

Bayan amsa tambayoyin Sanataoci 15 da Abdulrasheed Bawa yayi a zauren majalisar dattawa, majalisar ta amince da nadin sa sabon shugaban hukumar EFCC.

Sai da ya dauki Bawa awa biyu cur yana amsa tambayoyin sanatocin kama daga alakar sa da tsoffin shugabannin hukumar zuwa zargin harkallar da ake zaton ya tafka a lokacin da ya ke shugabantar hukumar a jihar Ribas.

Bawa ya ce wadannan zargi basu da tushe. Ya karyata su.

A karshe, majalisar ta amince da nadin sa shugaban hukumar.

Idan ba a manta ba, shugaba Muhammadu Buhari ya aika da sunan Bawa domin majalisar ta amince da nadin sa sabon shugaban hukumar EFCC makonni biyu da suka gabata.

Bawa shine mai karancin shekaru na farko da aka taba nadawa shugaban hukumar kuma ba dan sanda ba.

Tun farkon soma aukin sa dama a hukumar EFCC din ya fara aiki a matsayin karamin ma’aikaci a lokacin da Nuhu Ribadu ke shugabantar hukumar.

Share.

game da Author