A dalilin sace daliban makarantar kwana dake garin Kagara da aka yi a daren Talata gwamnatin jihar Neja ta rufe makarantun kwana dake kananan hukumomi hudu a jihar.
Gwamnan jihar Abubakar Sani ya bayyana haka ne ranar Laraba da yake ganawa da manema labarai a fadar gwamnati.
Gwamnati ta bada umurnin a rufe makarantun kwana dake kananan hukumomin Rafi, Mariga, Munya da Shiroro.
Sani-Bello ya ce gwamnati na kokarin ganin an ceto wadannan yaran makaranta na Kagara da mahara suka sace ba tare da an biya ko kwandala kudin fansa ba.
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya umurci jami’an tsaro da su yi gaggawan ceto wadannan dalibai da aka sace a jihar.
Idan ba a manta ba wannan jaridar ta buga labarin yadda ‘yan bindiga suka sace daliban makarantar a cikin dare Talata.
PREMIUM TIMES ta buga cewa maharan sun dira makarantar Kagara cikin dare inda suka fi karfin jami’an tsaron dake gadin makarantar sannan suka kutsa cikin makarantar suka yi awon gaba da ɗalibai da dama.
Wannan dauke ɗalibai da aka yi ya zo watanni uku bayan an sako daliban makarantar Kankara jihar Katsina, wanda suma mahara ne suka yi awon gaba da su.
Baya ga dalibai da ake kokarin cetowa akwai wasu matafiya har 30 da ‘yan bindiga suka sace su a hanyar zuwa Minna daga taron biki.
Maharan na bukatar aka wo musu naira miliyan 500, kafin su saki matafiyan.