Buhari ya umurci jami’an tsaro su gaggauta ceto daliban makarantar sakandaren Kagara

0

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya umurci jami’an tsaron su gaggauta ceto daliban makarantar sakandaren Kagara da aka yi garkuwa da su cikin daren Talata.

Shugaba Buhari ya umarci da a tura zaratan sojoji su fantsama wannan daji domin ceto wadannan ƴan makaranta.

Kakakin fadar shugaban kasa Garba Shehu ya sanar da haka a wata takarda da ya raba wa manema labarai ranar Laraba.

A dalilin wannan garkuwa da aka yi na ɗaliban makarantar kwana na Kagara gwamna Abubakar Bello ya umarci a rufe makarantun kwana dake kananan hukumomi 4 dake jihar.

Gwamnati ta bada umurnin a rufe makarantun kwana dake kananan hukumomin Rafi, Mariga, Munya da Shiroro.

Sani-Bello ya ce gwamnati na kokarin ganin an ceto wadannan yaran makaranta na Kagara da mahara suka sace ba tare da an biya ko kwandala kudin fansa ba.

Idan ba a manta ba wannan jaridar ta buga labarin yadda ‘yan bindiga suka sace daliban makarantar a cikin dare Talata.

PREMIUM TIMES ta buga cewa maharan sun dira makarantar Kagara cikin dare inda suka fi karfin jami’an tsaron dake gadin makarantar sannan suka kutsa cikin makarantar suka yi awon gaba da ɗalibai da dama.

Wannan dauke ɗalibai da aka yi ya zo watanni uku bayan an sako daliban makarantar Kankara jihar Katsina, wanda suma mahara ne suka yi awon gaba da su.

Baya ga dalibai da ake kokarin cetowa akwai wasu matafiya har 30 da ‘yan bindiga suka sace su a hanyar zuwa Minna daga taron biki.

Maharan na bukatar aka wo musu naira miliyan 500, kafin su saki matafiyan.

Share.

game da Author