GOBARA: Mutum uku sun mutu, rumfa 600 sun kone a sansanin ‘yan gudun hijra

0

Mutum uku sun mutu, rumfa 600 sun kone kurmus a gobarar da aka yi a sansanin ‘yan gudun hijra dake Maiduguri jihar Barno.

Gobarar ya auku ranar Talata da dare.

Shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Barno, SEMA Yabawa Kolo ta sanar da haka ranar Laraba.

“Mutane biyu da jariri daya ne suka mutu a wannan gobara. Sannan kuma ta babbake rumfar mutane 600 a sansanin ‘yan gudun hijiran.

Yabawa ta kara da cewa nan ba da dadewa ba hukumar SEMA za ta kawo abinci da sauran kaya na bukata domin tallafa wa wadanda gobarar ta lashe wa kaya.

Wannan bashine karon farko da gobara ke barkewa a Sansanonin ‘yan gudun hijra dake jihar Barno ba. Akan samu tashin gobara a sansanonin a baya.

Share.

game da Author