Yadda mahara suka waske da mahaifina, suka harbe yayyina biyu a Zariya – Usman

0

Da misalin karfe 10:30 na daren Lahadi mahara suka far wa gidan Wazirin Wusasa, Mohammed Aliyu dake unguwan Kuregu a Wusasa Zariya jihar Kaduna inda suka yi garkuwa da wazirin bayan sun kashe dan sa daya.

Mohammed wanda farfesa ne yana aiki a sashen koyar da harkokin noma a jami’ar Tafawa Balewa dake jihar Bauchi.

Daya daga cikin ‘ya’yan sa mai suna Usman Mohammed ya bayyana wa manema labarai cewa maharan sun harbi yayyin sa biyu inda nan take daya mai suna Abdulaziz ya mutu, dayan kuma Abubakar Kabir na kwance a asibiti a yanzu haka.

Usman ya bayyana cewa ko da ya dawo gida da dare kafin ya shiga can cikin gida sai yaji harbin bindiga a cikin gidan su. Da ya ji haka sai yayi lambo ya koma da baya bai shiga cikin gidan ba.

Mai unguwan Kuregu Ahmad Amfani ya bayyana wa manema labarai cewa mutane sun yi kokarin sanar da jami’an tsaro domin kawo musu dauki amma ba su zo da wuri ba har maharan suk yi abinda za su yi suka tafi.

Har yanzu rundunar ‘yan sanda ba ta ce komai ba kan abin amma kuma gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da aukuwar abin.

A wani takarda da aka raba wa manema labarai ranar Litini kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin gida, Samuel Aruwan ya shaida cewa mahara sun arce da farfesa Mohammed sannan sun kashe daya daga cikin ‘ya’yan sa.

Share.

game da Author